Jonathan zai yi jawabi a taron AfBA, Lauyoyin Afrika za su karrama shi a Niamey

Jonathan zai yi jawabi a taron AfBA, Lauyoyin Afrika za su karrama shi a Niamey

-An zabi Goodluck Jonathan ya yi jawabi a taron AfBA da za a shirya a 2021

-Kungiyar AfBA za ta karrama tsohon Shugaban Najeriyar da lambar girma

-Lauyoyin su na ganin Goodluck Jonathan ya na taka rawar gani a Nahiyar

Kungiyar lauyoyi na Afrika ta ce ta gama magana da wasu tsofaffin shugabannin kasashe da za su yi magana a wajen babban taron da za ta yi a 2021.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Alhamis cewa za ayi wannan taro ne a tsakiyar shekara mai zuwa.

Jaridar ta ce Goodluck Jonathan da wasu tsofaffin shugabannin kasar Afrika da su ka sauka daga mulki za su tofa albarkacin bakinsu a wannan taro.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar lauyoyin, Hannibal Uwaifo inda ya ce Dr. Denis Mukegwe ne zai zama babban mai jawabi.

KU KARANTA: Jonathan ya na cikin masu kokarin dinke barakar Gambiya

Taken wannan lacca da kungiyar ta AfBA za ta yi a shekara mai zuwa shi ne tsara yadda za a kawo sauyi a nahiyar Afrikar da ake fama da ta’addanci.

Hannibal Uwaifo ya ce za ayi wannan taro ne a birnin Niamye, kasar Jamhuriyyar Nijar. Ana sa ran cewa fiye da 4, 000 daga ko ina za su samu halarta.

Uwaifo ya ce Goodluck Jonathan ya na cikin wadanda za a karrama da lambar girma saboda gudumuwarsa a harkar shugabanci da mulkin farar hula.

Kungiyar lauyoyin ta ce tsohon shugaban na Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya na taka rawar gani wajen kawo cigaba a harkar damukaradiyya a Afrika.

KU KARANTA: Jonathan zai sake neman takara a 2023?

Jonathan zai yi jawabi a taron AfBA, Lauyoyin Afrika za su karrama shi a Niamey
Goodluck Jonathan da Patience Hoto: www.thebreakingtimes.com
Asali: UGC

Za a tattauna batutuwa a wajen taron, wanda su ka hada da; hakkin kare Bil Adama, dokar kasa, cin zarafin yara da mata, harkar zabe, kwadago da sauransu.

A shekarar 2018 an karrama tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan a wata Jami’a da ke Jihar Ribas saboda kokarin da yayi a tafiyar siyasar Najeriya.

Jami’ar ilmi ta Ignatius Ajuru ta Jihar Ribas ce ta ba tsohon Shugaba Goodluck Jonathan lambar yabo na gwarzon Damukaradiyya a Najeriya a wancan lokaci.

A 2015, gwamnatin Jonathan ta gudanar da zaben kwarai har ya rasa tazarce, bayan nan ya sauka daga karagar mulki, ya mikawa Jam’iyyar adawa mulkin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel