Talauci na kisa fiye da COVID-19, in ji Falana

Talauci na kisa fiye da COVID-19, in ji Falana

- Femi Falana a wata tattaunawa ta intanet ta ASCAB ta shirya ya bayyana cewa talauci yafi Coronavirus saurin kisa a Najeriya

- Yayin da gwamnati ke kokarin kawo rigakafin COVID-19, dole ta samar da hanyoyin kakkabe talauci da sauran cutuka da ke addabar talaka, a cewa Falana

- Ya kara da cewa gwamnati na bawa COVID-19 kulawa ne saboda ba cuta ce da ta shafi talaka ba sai dai masu arziki

Shugaban kungiyar Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond (ASCAB), Mista Femi Falana (SAN) ya ce talauci ya fi saurin kisa akan COVID-19, The Punch ruwaito.

Saboda haka, ya bayyana cewa yayin da gwamnati ke shirin siyo rigakafi don shawo kan cutar, to dole ne ta samar da hanyoyin da zata kawar da talauci ta kuma shawo kan sauran cutuka.

Talauci ta fi korona kisa, in ji Femi Falana
Talauci ta fi korona kisa, in ji Femi Falana. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook

Babban lauyan ya shaida haka ne a wata tattaunawar yanar gizo ranar Laraba mai taken, 'Ra'ayin al'umma kan dawowar COVID-19 a zango na biyu da kuma matsayar bangaren lafiya a Najeriya'.

"Akwai bukatar matakin gaggawa a bangaren lafiya, amma ba COVID-19 ce tafi damun mutane ba. Tsawon shekaru yanzu, mafi yawancin talakawa na fama da manyan cutuka. A 2018 hukumar lafiya ta duniya ta yi kiyasin cewa akwai akalla mutane 20,000 da ke mutuwa ko wanne sati a Najeriya wanda za a iya magance hakan idan da anbi matakan da suka dace.

"Baza ka hada wannan da annobar COVID-19 ba wanda ko mutane 50 ba sa mutuwa a sati ba", inji Falana.

Shugaban ASCAB din yayi bayanin cewa dalilin da ya sa aka fi maida hankali akan COVID-19 shi ne cutar ta na taba masu kudi.

KU KARANTA: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

Ya ce da wahala kaga ana mayar da hankali ga cutar da ta shafi iya talaka.

"Masu kudi da mulki sun kasa tsame kan su daga hadarin kamu wa da COVID-19, sai aka kirkiri dokar kulle akan talaka don su kare kansu, amma baza su saki wadataccen kudi ga bangaren lafiya ba.

"Dalilin haka, ma'aikatan lafiya da likitoci sun ga illa kuma sun sha wahala saboda rashin wadataccen kayan aiki tare da hadarin kamu wa da COVID-19. Likitoci 20 sun mutu saboda rashin kayan kare kai," a cewar Falana.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel