Sanusi II, Shekarau, Nasiru Ado sun yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwa a Kano

Sanusi II, Shekarau, Nasiru Ado sun yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwa a Kano

- Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wa Marigayi Majidadin Kano addu'o'i

- Hakimin kasar Madobi ya rasu ne a ranar Juma’a, bayan shekaru 60 a kan karaga

- Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana Marigayi Majidadi da Dattijon Hakimi

A wani faifen bidiyo, an ga tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya na yi wa al’umma ta’aziyyar rasuwar Mahaifin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

Malam Muhammadu Sanusi II ya ce ya samu labarin Allah ya yi wa Mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano watau Majidadin Kano kuma Hakimin Madobi rasuwa.

Tsohon Sarki Sanusi II ya ce: “Marigayi Hakimin Madobi (Musa Saleh Kwankwaso) Dattijo ne, wanda ya shafe sama da shekaru 60 ya na Dagaci, ya na Hakimi."

A bidiyon, Malam Sanusi II ya hada da addu’a: “Allah ya gafarta masa, Allah ya ba iyalinsa hakuri.”

KU KARANTA: Sarkin Kano ya kai wa Kwankwaso ziyara, ya yi masa ta’aziyya

“Dukkanin musulmi da su ka rasa ‘yanuwa, Allah ya gafarta masu.” Tsohon gwamnan na bankin CBN ya kara da rokon: “Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Amin.”

A karshe tsohon Sarkin ya yi addu’ar Allah ya tabbatar da alheri. Sannan ya bukaci ayi salati goma ga Manzon Allah da karatun wasu surori a madadin Marigayin.

Kamar yadda masoyan Mai martaban su ka bayyana a shafin Twitter, Malam Sanusi II ya yi wannan ta’aziyya ne tun ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba, 2020.

KU KARANTA: Buhari ya yi wa Kwankwaso ta'aziyyar Majidadi

Sanusi II, Shekarau, Nasiru Ado sun yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwa a Kano
Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero wajen gaisuwa Hoto: Twitter/SaifullahiHon
Source: Twitter

Ko da tsohon Sarkin bai samu ziyarar gidan makokin ba, Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ziyarci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi masa ta’aziyya.

A yau Laraba ne tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya je ya yi wa Rabiu Kwankwaso ta’aziyya na rashin da aka yi wa danginsu da daukacin Kano.

Musa Saleh Kwankwaso ya zama Hakimi ne tun kafin 'Ya 'yan Ado Bayero su zama Hakimai.

Alhaji Sabo Nanono, Hadi Sirika, Nasiru Gawuna, Nasiru Makoda, Usman Alhaji, Ramalan Yero, Ahmad Makarfi, Kabir Marafa, duk sun je sun mika gaisuwarsu.

Haka zalika Bashir Tofa, Naja'atu Mohammed, Buba Galadima, Nazif Gamawa da gwamna Bala Mohammed da wasunsu sun yi wa 'Dan siyasar gaisuwa a gida.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel