Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari

Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari

- Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce lokacin ya na kan kujerarsa, yana daukar matakai ne don cigaban kasa

- A cewarsa, har kin tabbatar da wasu mutane suka yi a kan kujerunsu saboda ba su tabbatar da nagartarsu ba, kuma sun yi hakan ne don cigaba

- A cewarsa, su na gayyatar shugabannin tsaro da sifeta janar don su tattauna da su don tabbatar da tsaron Najeriya ba don kansu ba

Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce lokacin yana kujerarsa, bai tabbatar da wasu daga cikin wadanda Shugaba Buhari ya nada ba, saboda bai amince da nagartarsu ba.

Saraki ya fadi hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake mayar da martani ga Momodu, mawallafin mujallar Ovation, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Momodu ya bayyana tsohon gwamnan Kwara a matsayin shugaban da yafi ko wanne shugaba kaifin tunani a Najeriya.

KU KARANTA: Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci

Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari
Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce lokacin yana shugabancin majalisar dattawa, su na daukar mataki ne saboda gaba daya kasa ba wai don farin cikinsu ba.

"Kamar yadda nake yawan fadi lokacin ina tare da shugaban kasa, muna daukar matakai ne saboda cigaban kasa, ba wai don son zuciyoyinmu ba.

"Bamu tabbatar da wasu a kan kujerunsu ba, saboda tsantsaininmu. Lokacin da muka gayyaci shugabannin tsaro da sifeta janar na 'yan sanda, mun yi hakan ne don samar da mafita ga matsalolin rashin tsaro a lokacin, ba wai don kanmu ba," yace.

KU KARANTA: Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 9 a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja yayin da suka yi musayar wuta da su a daren Litinin zuwa sa'o'in farkon ranar Talata, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar.

Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya sanar, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri ne da ke nuna cewa 'yan ta'addan suna kokarin matsawa daga yankin gabas na titin Abuja zuwa Kaduna zuwa yammaci tare da shanun da suka sata.

"Makiyayan wadanda aka sacewa shanun ne suka sanar da dakarun sojin inda suka dauka mataki," Aruwan yace a wata takarda da ya fitar ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel