Za mu yi kokarin sa ido a kan farashin kayan abinci a 2021 Inji Buhari

Za mu yi kokarin sa ido a kan farashin kayan abinci a 2021 Inji Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi maganin tsadar kayan abinci

- Buhari ya zauna da Masu bada shawara kan harkar tattalin arziki a Aso Villa

- Shugaban Najeriyar ya ce an samu nasarori a bangaren noma a gwamnatinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta rika lura da yadda farashin kayan abinci su ke tashi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Mai girma Muhammadu Buhari ya na alkawarin ganin kaya ba su yi mahaukaciyar tsada a shekarar badi ba.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, 2020, lokacin da ya gana da masu ba shi shawara a kan tattali.

Buhari ya kuma bada umarni ga babban bankin Najeriya ya daina bada kudi ga mutane domin shigo da abinci cikin gida daga kasashen waje.

KU KARANTA: Yadda Minista ya jefa dinbin Matasa cikin zaman kashe-wando

Dalilin shugaban kasar shi ne jihohi bakwai su na noman shinkafa, don haka babu bukatar kawo abin da Najeriya za ta iya nomawa kanta da kanta.

Wannan alkawari ya zo ne a lokacin da saura sa’o’i kadan a shiga sabuwar shekara, inda a shekarar bana aka yi fama da tsadar abinci a kasar.

A wajen wannan taro da shugaban kasar ya yi da gawurtattun masana tattalin, ya bayyana masu irin nasarorin da kasar ta samu a bangaren noma.

Buhari ya ce a yadda annobar COVID-19 ta daburtawa kasashe lissafi, da Najeriya ta shiga matsala ba don ta rungumi sha’anin noma gadan-gadan ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta shigo da tsarin da yaran Arewa za su ci moriya

Za mu yi kokarin sa ido a kan farashin kayan abinci a 2021 Inji Buhari
Buhari ya sa kafar wando daya da tashin kudin abinci Hoto: www.channelstv.com
Source: UGC

An yi wannan zama ne a Aso Villa domin ganin yadda za a shawo kan tattalin arzikin kasar. Mataimakin shugaban kasaYemi Osinbajo ya na wurin.

Wasu jami'an gwamnati irinsu Zainab Ahmed, Sadiya Umar Faruk duk sun samu halarta.

A jiya kun ji cewa a jawabin da shugaban kasa Buhari ya gabatar yayin zama da kwamitin da ke ba shi shawara ya ce rufe iyakoki ya taimaki Najeriya.

An rahoto shugaban kasar ya na mai cewa: "Ba don mun rungumi noma, mun rufe iyakokinmu ba, da mun shiga wani mawuyacin halin da ya fi na yanzu."

Buhari ya bukaci 'yan Nigeria su rungumi harkar gona, su daina dogara da arzikin man fetur.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel