COVID-19: ‘Yan damfara sun kusa yin gaba da kudin kwangilar tsummar rufe fuska
- Jami’an lafiya a Jamus sun aika kudi da nufin shigo da tsummar rufe fuska
- Interpol sun gano shirin awon gaba da wannan makudan kudi da aka bada
- ‘Yan damfara sunyi nufin karkatar da kudin zuwa wani asusu da ke Najeriya
Jaridar Punch ta ce hukumar nan ta International Criminal Police Organisation ta ‘yan sandan Duniya ta gano wata badakalar COVID-19 a Najeriya.
Hukumar da aka fi sani da Interpol ta gano wata sata ta fam €500,000 da aka tafka ta Najeriya.
Interpol ta fitar da jawabi mai taken ‘Unmasked: International COVID-19 fraud exposed’ a shafinta na yanar gizo a ranar 29 ga watan Disamba, 2020.
Kamar yadda jawabin ya bayyana, an gano wani shiri da aka shigo da shi na satar dukiyar jama’a ta hanyar damfara, zamba cikin aminci da email.
KU KARANTA: Hadimin Aisha Buhari ya gagara bayyana inda ta shige
An binciko wannan barna ne a kasashen Jamus, Ireland da Holland, tare da hadin-gwiwar Interpol.
Jawabin ya ce: “A tsakiyar watan Maris a lokacin da ake rufe wasu kasashe saboda annobar Coronavirus, jami’an lafiyan kasar Jamus sun tuntubi wasu kamfanoni a Zurich da Hamburg su yi masu tsummar rufe fuska na fam miliyan €15 saboda karancin kayan asibiti.”
“An fara ne daga sakon Email zuwa shafin yanar gizo wanda ya yi kama da na gaske a kasar Sifen.” Hukumomi sun dauka su na magana ne da kamfanin gaske.
Wannan cinikin bai yiwu ba, sai aka hada su da wani kamfani na dabam a kasar Ireland. Ashe a sanadiyyar haka aka kutsa cikin akwatin Email din hukumomin.
KU KARANTA: Abubuwan da su ka girgiza Duniya cikin wannan shekara
Ana haka ne aka bukaci a tura fam miliyan 1.5, daga baya aka gano cewa kudin sun shiga hannun ‘yan damfara, nan take sai aka yi maza aka tuntubi jami'an Interpol.
Interpol ta gano duka wannan 880,000 da aka aika, daga ciki an tura 500,000 zuwa kasar Ingila, inda aka shirya aika duka kudin nan zuwa wani asusu da ke Najeriya.
A jiya ne PTF ya bada sanarwar cewa za a rika yi wa mutane gwajin kwayar COVID-19 a filin jirgin sama kafin su shigo Najeriya domin takaita yaduwar wannan cuta.
Kasashen da kwamitin PTF ya wajabtawa yin gwajin COVID-19 su ne Ingila da kuma Birtaniya.
Sai an tabbatar da lafiyar duk wanda zai shigo Najeriya daga kasashen nan biyu. Hakan na zuwa ne bayan an samu barkewar wani sabon nau'in COVID-19 daga Landan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng