Buhari ya aikewa Kwankwaso sakon ta'ziyyar rasuwan mahaifinsa, Makaman Karaye
- Allah ya yiwa mahaifin babban jagoran darikar Kwankwasiyya rasuwa
- An yi jana'izarsa bayan Sallar Juma'a a garin Kano
- Buhari ya siffanta marigayin matsayin mutum mai saukin sauki da tawali'u
Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa rasuwasr mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh.
Shugaba Buhari, a sakon da ya aike ranar Juma'a yace Najeriya ta yi rashin daya daga cikin masu sarautar gargajiya dake da mutunci.
Buhari a sakon da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya saki, ya ce ba za'a iya mantawa da gudunmuwar da mahaifin Kwankwaso ya bada ba wajen hadin kan al'umma da zaman lafiya.
A cewar Buhari, "marigayi Salen mutum ne mai kyawun hali, mai tawali'u da saukin kai.
"Ina amfani da wannan damar wajen jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, gwamnatin jihar Kano, da masarautar Kano bisa mutuwar hakimin."
"Allah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya azurtashi da Aljannah, Amin,"
KU KARANTA: Yariman Saudiyya, MBS, ya karbi alluran rigakafin cutar Korona
An gudanar da jana'izar makaman Karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.
BBC Hausa ta ruwaito cewa an yi jana'izarsa ne a harabar masallacin gidan Rabiu Kwankwaso da ke unguwar Bompai a jihar Kano.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.
KARANTA: Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng