Da Mun Kasance Cikin Matsala Da Bamu Kulle Iyakokin Kasarmu Ba - Shugaba Buhari

Da Mun Kasance Cikin Matsala Da Bamu Kulle Iyakokin Kasarmu Ba - Shugaba Buhari

- Buhari ya bayyana ribar da Najeriya ta samu sakamakon rufe iyakoki

- Ya jaddada umurnin hana shigo da kayan abinci daga kasashen waje

- Shugaban kasan ya yi kira ga yan Najeriya su koma goma kuma su daina dogara kan arzikin man fetur

Gwamnatin Tarayya a watan Agustan 2019 ta rufe kan iyakokinta na kasa don takaita shigo da magunguna da kananan makamai, da kayan gona a cikin kasar daga makwabta kasashen yammacin Afirka, Channels Tv ta Ruwaito.

Duk da haka, Shugaba Buhari ya ba da umarnin sake bude kan iyakokin kasar a ranar 16 ga watan Disamba, bayan an rufe shi sama da shekara guda.

Da yake magana a zamnasa tare da masu bashi shawaraa bangaren Tattalin Arziki wanda aka yi a ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa a Abuja, Buhari ya ba da umarnin cewa Babban Bankin Najeriya “kada ya ba da kudi don shigo da abinci. Tuni kusan jihohi bakwai ke samar da dukkan shinkafar da muke buƙata. Dole ne mu ci abin da muka samar. ”

“Ka yi tunanin abin da zai faru idan ba mu ƙarfafa harkar noma ba kuma muka rufe kan iyakoki. Da mun kasance cikin matsala, ”inji shi.

“Za mu ci gaba da karfafa wa mutanenmu gwiwa su koma gona. An cusa mana ra'ayin cewa muna da arzikin mai, muna barin kasa zuwa birni don arzikin mai.

“Mun dawo noman yanzu. Bai kamata mu rasa damar da za mu kawowa mutanenmu sauki ba. ”

Shugaba Buhari ya kuma jaddada mahimmancin aikin noma wajen dawo da tattalin arzikin kasar, inda ya kara da cewa dole ne a samar da matakan takaita hauhawar farashin kayayyaki.

KU KARANTA: Gobe shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021

Da Mun Kasance Cikin Matsala Da Bamu Kulle Iyakokin Kasarmu Ba - Shugaba Buhari
Da Mun Kasance Cikin Matsala Da Bamu Kulle Iyakokin Kasarmu Ba - Shugaba Buhari
Source: Facebook

DUBA NAN: Kuma dai: Kimanin mutane 750 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

A bangare guda, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Nigeria (NCDC) ta yi gargadin cewa za'a sha wahala a cikin watan Janairu mai zuwa saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da za'a fuskanta.

NCDC ta ce za'a fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da kwayar cutar za ta harba saboda yadda jama'a suka yi burus da matakan kiyayewa yayin bukukuwan hutun da aka samu, kamar yadda The Nation ta rawaito.

A cewar NCDC, makon da ya gabata ya kasance daga cikin mafi ban tsoro saboda tashin gwauron zabi da alkaluman mutanen da suka kamu da cutar ya yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel