Kuma dai: Kimanin mutane 750 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

Kuma dai: Kimanin mutane 750 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

- A ranar Litinin an dan samu sauki, mutane 397 suka kamu da cutar Korona

- Amma ranar Talata bata yi kyau ba yayinda aka koma inda aka fito

- Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasar Amurka da Ingila ba

Mutane 749 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 85,560 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 85,000 da suka kamu, an sallami 71,937 yayinda 1267 suka rigamu gidan gaskiya.

Wani sabon nauyin cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.

KU KARANTA: Za mu yi kokarin sa ido a kan farashin kayan abinci a 2021 Inji Buhari

Kuma dai: Kimanin mutane 750 sun kamu da cutar Korona ranar Talata
Kuma dai: Kimanin mutane 750 sun kamu da cutar Korona ranar Talata Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

KU DUBA: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria a kan Korona 2.0

Ga adadin jiha-jiha:

Lagos-299

Plateau-131

Kaduna-83

FCT-74

Kwara-35

Sokoto-26

Edo-18

Kano-17

Katsina-16

Delta-11

Nasarawa-10

Ondo-9

Bauchi-9

Rivers-5

Akwa Ibom-3

Jigawa-1

Osun-1

Ekiti-1

A bangare guda, ma'aikatar kula da birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce Likitoci 476 ne suka kamu da cutar Korona tun lokacin bullarta a watan Febrairu, 2020 a Najeriya.

Anthony Ogunleye, Sakataren yada labaran Ministan FCT, Mohammed Musa Bello, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata a Abuja.

"Tun lokacin da aka samu bullar cutar COVID-19 a FCT, ma'aikatan lafiya 476, suka kamu da cutar. Wannan ya hada da Likitoci, ma'aikatan jinya, masu bada magani, masu gwaji, direbobi da dss," Ogunleye yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel