Gobe shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021

Gobe shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021

- Ana saura kwana daya karshen shekara, Buhari bai rattafa hannu kan kasafin kudi ba

- Amma majiyoyi daga cikin fadar shugaban sun bayyana cewa lallai kafin karshen shekara zai rattafa

- Majalisar dokoki ta amince da kasafin kudin 13.5tr kwanaki 9 da suka gabata

Muddin ba'a samu canji ba, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 gobe Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2021, PUNCH ta ruwaito.

Gwamnati Buhari ta bayyana niyyarta na tabbatar da cewa an kammala komai na kasafin kudi kafin karshen shekara saboda a rika aiwatar da kasafin daga Junairu zuwa Disamba.

Kuma haka akayi a kasafin kudin 2020 wanda Buhari ya rattafa hannu ranar 17 ga Disamba, 2019.

Ana kyautata zato gobe ranan karshen shekarar nan shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Talata.

"Muddin ba'a samu wani canji ba, shugaban kasa zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 ranar Alhamis," yace.

"Babu dai wani alaman za'a samu wani matsala ko canji,"

KU KARANTA: Kuma dai: Kimanin mutane 750 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

Gobe shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Gobe shugaba Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za mu yi kokarin sa ido a kan farashin kayan abinci a 2021 Inji Buhari

A ka'ida idan yan majalisar dokoki suka amince da kasafin kudin kuma suka kai fadar shugaban kasa, za'a gayyaci ministoci su duba.

Manufar haka shine tabbatar da cewa irin sauye-sauyen da yan majalisan suka yiwa kasafin kudin.

A ranar 21 ga wata, majalisar dattawa Najeriya ta amince da kasafin kudin N13.588 tiriliyan na shekarar 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar watanni biyu baya.

Hakan ya biyo bayan kammala aikin da kwamitin lissafe-lissafen kasafin kudi da tayi kan kasafin kudin.

Shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin, ya gabatar da daftarin kasafin kudin a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020.

Yan majalisar sun yi karin sama da biliyan 500 kan abinda shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng