Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria a kan Korona 2.0

Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria a kan Korona 2.0

- NCDC, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa, ta ce 'yan Nigeria sun yi uwar watsi da matakan dakile yaduwar annobar korona

- Shuagaban NCDC ya ce 'yan Nigeria su shirya domin za'a fuskanc hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona daga satin nan

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Nigeria (NCDC) ta yi gargadin cewa za'a sha wahala a cikin watan Janairu mai zuwa saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da za'a fuskanta.

NCDC ta ce za'a fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da kwayar cutar za ta harba saboda yadda jama'a suka yi burus da matakan kiyayewa yayin bukukuwan hutun da aka samu, kamar yadda The Nation ta rawaito.

A cewar NCDC, makon da ya gabata ya kasance daga cikin mafi ban tsoro saboda tashin gwauron zabi da alkaluman mutanen da suka kamu da cutar ya yi.

KARANTA: Pantami Vs Dabiri, Malami Vs Magu da wasu sabani 3 da aka samu tsakanin hadiman Buhari

A saboda haka, cibiyar ta gargadi 'yan Nigeria tare da yi musu tunin cewa su shirya girbar abinda suka shuka tunda suka yi watsi da dukkan sharuda da matankan kiyayewa yayin hutun bukukuwan kirsimeti da karshen shekara.

Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria a kan Korona 2.0
Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria a kan Korona 2.0 @NCDC
Asali: Twitter

Darekta Janar na NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu, shine ya fadi hakan a Abuja yayin taron kwamitin PTF akan korona na ranar Talata.

KARANTA: Buhari: Rufe boda alheri ne, ku rungumi noma, ba zamu ware kudi don shigo da abinci ba

"Mun fuskanci sati mafi muni tun bayan barkewar annobar korona, amma sai gashi cikin makon da ya biyo bayansa, jama'a sun yi watsi da duk wasu matakan kiyayewa.

"Ga hotuna da bidiyon taron jama'a a wurin shagulgulan biki suna ta yawo a dandalin sada zumunta, abin haushi da tayar da hankali.

"Za'a ji jiki a watan Janairu, babu wani abin mamaki idan an fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da zasu kamu da kwayar cutar korona sakamakon cudanya da saba ka'idojin da gwamnati ta gindaya," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fidda sanarwar ƙaryata neman afuwar Shugaba Buhari bisa gayyatarsa ya gurfana gaban majalisar don bayani kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke fitarwa kan cewar ƴan majalisar za su roƙi afuwar Shugaban ƙasa bayan sun amince da ƙudirin gayyatarsa, kamar yadda BBC ta wallafa.

Wasu ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka nemi a gayyato shugaba Buhari don ya yi bayani akan halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel