Jerin wayoyin da manhajar WhatsApp za ta daina aiki kansu a 2021

Jerin wayoyin da manhajar WhatsApp za ta daina aiki kansu a 2021

- Miliyoyin wayoyi a fadin duniya na gab da daina WhatsApp a sabuwar shekara

- Manhajar WhatsApp ta shahara cikin al'umma inda kusan kowa na amfani da ita

- A cewar Wikipedia, sama da mutane bilyan 2 na amfani da WhatsApp a fadin duniya

Wani sabon tsarin da kamfanin WhatsApp ke shirin kawowa a 2021 zai hana manhajar kamfanin aiki kan miliyoyin waya a fadin duniya fari daga ranar 1 ga Junairu, 2021.

Vanguard ta tattaro wasu wayoyi da manhajar za ta daina aiki kuma hakan zai tilastawa masu irin wayoyin kara girman kwakwalwar aiki (OS) ko kuma siyan sabon waya.

Ga jerin wayoyin da WhatsApp zata daina aiki a 2021:

Apple iPhone 1-4

Samsung Galaxy S2

HTC Desire

LG Optimus Black

Motorola Droid Razr

Duk wayar Android da aka fitar kafin 2010.

KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila

Jerin wayoyin da manhajar WhatsApp za ta daina aikin kansu a 2021
Jerin wayoyin da manhajar WhatsApp za ta daina aikin kansu a 2021
Source: UGC

KU DUBA: Kasar Afirka ta Kudu ta haramta siyar da giya tare da wajabta amfani da takunkumin fuska

Wayoyin da zasu bukaci karin girman kwakwalwar aiki (OS) zuwa akalla iOS 9 ko Andriod 4.0.3

Apple iPhone 4S

iPhone 5

iPhone 5S

iPhone 6

iPhone 6S

Samsung Galaxy S3

Samsung Galaxy Note

HTC Sensation

HTC Thunderbolt

LG Lucid

Motorola Droid 4

Sony Xperia Pro

A wani labarin kuwa, gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su daina cire N20 yayinda mutane ke kokarin duba lambar katin zama dan kasa da akafi sani da NIN.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya bada umurnin a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Sakamakon wannan umurni, yan Najeriya zasu iya samun lambar NIN kyauta idan suka danna *346# a wayansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel