Yanzu-yanzu: Pantami ya umurci kamfanonin sadarwa su daina cire N20 don duba lamban katin zama dan kasa NIN

Yanzu-yanzu: Pantami ya umurci kamfanonin sadarwa su daina cire N20 don duba lamban katin zama dan kasa NIN

- Bayan kukan yan Najeriya kan kudi N20 da kamfanonin sadarwa ke yi, Pantami ya yi umurni

- Yanzu yan Najeriya zasu iya samun lambobin NIN cikin kwanciyar hankali

- Gwamnati ta bada makonni biyu don kowa ya hada lambar wayansa da na NIN

Gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su daina cire N20 yayinda mutane ke kokarin duba lambar katin zama dan kasa da akafi sani da NIN.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya bada umurnin a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Sakamakon wannan umurni, yan Najeriya zasu iya samun lambar NIN kyauta idan suka danna *346# a wayansu.

Wani sashen jawabin yace: "Sakamakon wannan yafuwa, mutane zasu iya amfani da *346# domin samun lambar NIN dinsu kyauta."

"Minista na godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki kuma yana kira da su cigaba da hakuri da sadaukar da kai don dadin kasa."

KU KARANTA: Mun bi umurnin Buhari, mun bude iyakoki: Hukumar shiga da fice

Yanzu-yanzu: Pantami ya umurci kamfanonin sadarwa su daina cire N20 don duba lamban katin zama dan kasa NIN
Yanzu-yanzu: Pantami ya umurci kamfanonin sadarwa su daina cire N20 don duba lamban katin zama dan kasa NIN
Asali: Original

KU DUBA: Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC

Mun kawo muku cewa gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su rufe layin wayan duka wanda bai hada layinsa da lambar katin zama dan kasa nan da ranar 30 ga Disamba, 2020.

Wannan umurni ya biyo bayan ganawar gaggawan masu ruwa da tsaki a sashen sadarwa da Minista, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami ya shirya ranar Litinin, 14 ga Disamba, 2020.

Bayan ganawar, an yi ittifakin cewa fari daga ranar Alhamis, 16 ga Disamba, 2020, dukkan kamfanonin sadarwa su bukaci mutane su hada layukan wayansu da lambar katin zama dan kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel