Kasar Afirka ta Kudu ta haramta siyar da giya tare da wajabta amfani da takunkumin fuska

Kasar Afirka ta Kudu ta haramta siyar da giya tare da wajabta amfani da takunkumin fuska

- Shugaban Afirka ta Kudu ya haramta siyar da giya tare da wajabta amfani da takunkumin fuska a cikin taron jama'a

- Shugaban ya ayyana dokar ne bayan da kasar ta zama ta farko a nahiyar Afirka da ta samu sama da mutane miliyan daya da suka kamu da Coronavirus

- Idan bamu dauki mataki ba, kuma tsatsauran mataki, zamu samu ninkin karuwar masu cutar fiye da zangon farko na annobar kuma dubban mutane zasu rasa rayukansu

Shugaba Cyril Ramaphosa a ranar Litinin ya sanar da sabuwar dokar hana siyar da giya ya kuma ce wajibi ne amfani da takunkumin fuska a wajen taron jama'a bayan Kasar Afirka ta Kudu ta zama ta farko a nahiyar Afirka da ta kai mutane miliyan daya da suka kamu da Coronavirus.

Ramaphosa ya zartar da sababbin sharadai saboda "yawan karuwar" masu cutar, musamman ganin cewa barkewar cutar karo na biyu na iya zama mai munin gaske, Channels tv ta ruwaito.

Kasar Afirka Ta Kudu ta haramta siyar da giya tare da wajabta amfani da takunkumin fuska
Kasar Afirka Ta Kudu ta haramta siyar da giya tare da wajabta amfani da takunkumin fuska. @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

Ya dora alhakin yawan karuwar cutar ga yawan taron shagulgula da kuma rashin sa idanu lokacin hutu.

"Mun janye matakan mu, kuma abin takaici yanzu muna girbar abin da muka shuka," shugaban kasar ya bayyana a wata hirar gidan talabijin.

Kasar da tafi yawan samun masu cutar Coronavirus a Afirka ta haramta siyar da giya a can baya cikin watan Mayu lokacin da ake fama da mummunar annobar a karon farko.

Ramaphosa ya ce alkalumma sun nuna cewa "yawan ta'ammali da giya" ya janyo karuwar samun rahotannin mabambantan jinyoyi a asibitoci.

Lamarin ya janyo mana cikowar wuraren kula da lafiya wanda dama can a matse ake, ya ce dokar zata fara aiki a tsakiyar dare.

KU KARANTA: Nasiru Kachalla: An kashe ƙasurgumin dan bindiga a dajin Kaduna

Ya ce fiye da ma'aikatan lafiya 41,000 ne suka kamu da cutar COVID-19 daga lokacin da aka fara yaki da ita a kasar.

Dokar kullen kasar yanzu zata dinga aiki daga 9:00 zuwa 11:00 na dare sai kuma shaguna da gidajen cin abinci da wuraren shan barasa da zasu dinga rufewa 8:00 na dare.

Dukkanin taruwar mutane a cikin wani guri ko a waje haramtacce ne tsawon sati biyu in banda taron jana'iza wanda za a takaita shi zuwa mutum 50.

Afirka ta Kudu ta haura rahotannin Coronavirus miliyan daya a ranar Lahadi, kuma kusan mutum 27,000 sun mutu saboda cutar.

"Dole sai mun dauki mataki yanzu matakin da ya dace, sababbin wanda ke daukar cutar zai zarce yadda muka samu a zangon farko na cutar kuma dubban mutane za su rasa rayukansu," inji Ramaphosa.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164