Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila
- Tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a kasar Isra'ila bayan da aka yi masa allurar rigakafin korona
- Tsohon tuni yake fama da ciwon zuciya, kuma bincike ya nuna cewa ciwon zuciyan ne ya kashe shi
- Ya fadi bai san inda kan shi yake ba bayan sa'o'i biyu da yi masa allurar a asibitin Clalit da ke kasar
Wani tsoho mai shekaru 75 daga arewacin Isra'ila ya rasu sakamakon ciwon zuciya bayan sa'o'i biyu da aka yi masa allurar rigakafin cutar korona a ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, ma'aikatar lafiya ta tabbatar.
Tuni mutumin yana da ciwon zuciya kuma ya kasance yana wahala da ita, ma'aikatar lafiyan ta tabbatar.
Chezy Levy, darakta janar na ma'aikatar lafiya ya kaddamar da bincike a kan lamarin.
KU KARANTA: Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade
Mutumin ya karba riga-kafin wurin karfe 8: 30 na safe a asibitin Clalit. Ya jira na gajeren lokaci kafin a bar shi ya tafi gida lafiya kalau.
Kamar yadda Jerusalem Post ta tabbatar, mutumin ya fadi bai san inda kan shi yake ba kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa sakamakon ciwon zuciya.
Levy ya ce binciken farko da suka fara bai nuna wata alaka tsakanin mutuwar mutumin ba da rigakafin.
A kalla kasar Isra'ila ta yi wa mutum 380,000 allurar rigakafin cutar korona.
KU KARANTA: Gara in yi wufff in shige a mata ta 7 da in yi alakar banza, 'Yar kasuwa tare da Ned Nwoko
A wani labari na daban, Farfesa Yusuf Turaki ya ja kunne inda yace akwai yuwuwar Najeriya ta tarwatse a kowanne lokaci daga yanzu matukar aka cigaba da amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999.
A wata hira da yayi da jaridar The Sun, farfesan ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da abinda ba zai kai kasar nan inda ake tsammani ba.
Turaki ya ce babu shakka kundin tsarin mulkin kasar nan yana daga cikin dalilan da suka hana kasar nan cigaba duk da shekaru 60 da tayi da samun 'yancin kai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng