Garkuwa da mutane: Hira da wani Mutumi da aka sace a kan hanyar Birnin Gwari

Garkuwa da mutane: Hira da wani Mutumi da aka sace a kan hanyar Birnin Gwari

-Wani da ya fada hannun ‘Yan bindiga ya bada labarin abin da ya faru da su

-Wannan mutumi ya ce an bukaci 50m a hannunsa, amma N4m ta fito da shi

-Da yake tsare, wannan mutum ya hadu da Malamin ABU Zaria da aka dauke

Wani mazaunin jihar Kaduna da ya yi tsawon kwanaki 12 a hannun masu garkuwa da mutane ya bayyanawa jaridar Daily Trust irin abin da ya faru da shi.

Wannan Bawan Allah ya bada labarin yadda ya hadu da malamin jami’ar ABU Zaria, Dr. Ibrahim Bako, wanda aka tsare a lokacin (yanzu ya samu ‘yanci).

“Ina tafiya ni kadai a cikin mota a hanyar Kaduna-Birnin Gwari, bayan an wuce Buruku, kusa da Rumanan Gwari, sai ‘yan bindiga su ka bude mani wuta.”

A cewarsa, daga nan aka dauke shi zuwa cikin daji, su ka yi tafiyar kusan kilomita uku, sai su ka hau babur, su kayi doguwar tafiya zuwa inda aka tsare su.

KU KARANTA: An yi garkuwa da wadanda su ka dauko gawa a Birnin Gwari

A nan ne fa aka yi wa wannan mutumi tare da sauran wadanda aka kama mummunan bugu domin su yi maza su fadi abubuwan da su ka mallaka a Duniya.

A game da adadin ‘yan bindigan, sai ya ce: “Su na da yawa, sun haura 20, akwai manya da kananansu.”

Sun ce mani: “Idan gwamnati suna son zaman lafiya, dole su gane cewa su ‘Yan Najeriya ne, sai jami’an tsaro su yi sulhu da su, amma ba a rika kiransu miyagu ba.”

Daga cikin wadanda aka kashe akwai wanda aka gaza samun lambar wayar ‘yanuwansa, akwai kuma wanda ya yi masu tayin N10, 000 domin a sake shi.

KU KARANTA: Mutane 23 sun mutu, 22 sun raunata bayan faduwar mota

Garkuwa da mutane: Hira da wani Mutumi da aka sace a kan hanyar Birnin Gwari
Shugaban 'Yan Sanda na kasa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Farfesan da aka sace a ABU Zaria yana cikin wadanda wannan mutumi ya hadu da su a dajin. ‘Yan bindigan sun ki karbar N2m, su ka rantse sai an basu N10m.

Tun ana cewa a kawo miliyan 50, aka yi ta magana har aka zo kan miliyan 4, ‘yanuwan wannan mutumi su na bada wannan kudi, aka fito da shi, aka sake shi.

Dazu kun ji cewa wasu 'yan fashi da makami sun kai hari a garuruwa shida da ke jihar Katsina, sun yi garkuwa da mutane 50 ciki har da wasu sababbin ma'aurata.

Rahotanni sun bayyana cew har ila yau mutum biyu sun rasa rayukansu a hannun miyagun.

Bayan haka, 'yan bindigan sun yi sace sace a gidajen jama’a yayin da su ka kai farmakin a garuruwan Daurawa, Kasai, Biya-ka-Kwana, Bakon Zabo da sauransu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel