Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a Katsina, sun yi garkuwa da mutum 50 harda sabbin ma’aurata

Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a Katsina, sun yi garkuwa da mutum 50 harda sabbin ma’aurata

- Wasu bayin Allah yan Najeriya na a hannun yan bindiga yanzu haka a jihar Katsina

- Har ila yau mutum biyu sun rasa rayukansu a hannun miyagun

- Yan bindigan sun kuma yi sace sace a gidajen jama’a a yayinda suka kai mamayar da daddare

Wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun jefa wasu garuruwan Katsina cikin bakin ciki bayan sun yi garkuwa da kimanin mutane 50.

Yan fashin wadanda suka kai hari kan al’umman sun kuma kashe mutum biyu a yayin mamayar da suka kai yankin Batsari da ke jihar Katsina a karshen mako.

Wasu daga cikin garuruwan da suka kai hari sun hada da Daurawa, Kasai, Biya-ka-Kwana, Bakon Zabo, Tudun Modi, Watangadiya da sauransu, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a Katsina, sun yi garkuwa da mutum 50 harda sabbin ma’aurata
Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a Katsina, sun yi garkuwa da mutum 50 harda sabbin ma’aurata Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta nemi a kama Kukah sannan a hukunta shi kan furucinsa game da Buhari

A garin Rumka, an kashe Sama’ila Supa, kawun wani dan majalisa mai wakiltan Safana a majalisar dokokin jihar Katsina.

Dan majalisar, Abduljalal Haruna, ya ce yan bindigan sun kashe kawun nasa a lokacin da ya nuna turjiya da suka yi yunkurin garkuwa da shi.

Ya ce:

“Duk wadannan abubuwa na faruwa ne duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin da aka kashe kawun nawa. Tazarar da ke tsakanin wajen da jami’an tsaron da inda yan bindigar suka aiwatar da ta’asarsu bai fi kilomita biyar ba.”

A halin da ake ciki, kakakin yan sandan jihar Katsina, Gambo lsah, ya ce jami’an yan sanda na iya bakin kokarinsu don kare garuruwan.

KU KARANTA KUMA: Daruruwan mutane sun tsere yayinda dakarun soji ke fafatawa da Boko Haram a kauyukan Borno

A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a daren Lahadi sun kashe shugaban kungiyar 'yan sintiri a garin Maigora a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, Malam Ummaru Balli.

Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum takwas yayin harin da suka kai a kauyen Rimi da ke karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.

An gano cewa Mallam Balli ya jagoranci wasu 'yan sintiri zuwa Rimi domin su taka wa 'yan bindigan da suka kai hari a Rimi birki a dare da abin ya faru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel