Kebbi: Mutane 23 sun mutu, 22 sun raunata bayan faduwar babbar motar shanu a hanyar zuwa Legas
- Wata babbar motar dako makare da shanu da mutane ta yi hatsari a yankin karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja
- Babbar motar ta taso ne daga garin Dadin Kowa da ke yankin jihar Kebbi
- Mutum 23 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mutane 22 suka samu raunuka sakamakon afkuwar hatsarin
Mutane 23 sun rasa rayukansu sanadiyyar haɗarin motar shanu wadda ke ɗauke da shanu da ƙarin lodin mutane 45 a Mokwa da ke Jihar Niger.
Motar ta taso daga jihar Kebbi ɗauke da ɗimbin shanu da mutane 45 a cakude a cikinta, kamar yadda PM News ta rawaito.
Rahotanni daga Rundunar ƴansandan jihar Niger sun ce motar ta ƙwace daga hannun matuƙinta kuma ta afka cikin jeji.
Haɗarin ya afku ne da misaƙin ƙarfe 05:00 a tsakanin titin Bokani zuwa Makera a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja kamar yadda kwamishinan ƴansanda jihar, Mista Adamu Usman, ya bayyana.
Usman ya ce motar mai rijista da lambar mallaka kamar haka: BBJ 666 XA ta taho ne daga Daɗin Kowa inda ta nufi jihar Legas.
Ya ce an kai gawarwakin matattun asibitin Mokwa don binciken gawa. Sannan an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin domin duba lafiyarsu.
Usman ya ɗora alhakin haɗarin motar kan ƙwacewar ragamar tuƙi daga hannun direbar motar.
Ya kuma koka akan rashin bin doka da ƙa'idar hanya da direbobi ke ƙin bi ko bijerewa.
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Ahmodu Mohammed, shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Kampala a Bosson, jihar Neja, ya rasa ransa sakamakon harin 'yan bindiga.
Wasu 'yan bindiga, kimanin su goma sha biyar, sun kai hari gidan Mohammed da tsakar daren ranar Juma'a.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da 'yammata uku, 'ya'yan Mohammed, bayan sun kashe shi.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng