Birnin Gwari: An yi garkuwa da wadanda su ka dauko Mamaci daga asibitin Shika

Birnin Gwari: An yi garkuwa da wadanda su ka dauko Mamaci daga asibitin Shika

A halin yanzu da satar jama’a ta zama ruwan dare, mun samu wani mummunan labari na wasu Bayin Allah da aka sace. Da alamu za a bukaci su biya kudin fansa kafin a sake su.

Hanyar Birnin Gwari a jihar Kaduna, ta zama sansanin masu garkuwa da mutane tun ba yau ba. Wannan ne ma ya sa mutane su ke kauracewa wannan daji mai matukar hadari.

Kwanan nan mu ka samu labari cewa an sace wasu Matasa har hudu a wannan hanya. Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan Bayin Allah su na dauke ne da gawar tsohonsu.

Masu garkuwa da mutanen sun tare su ne gaba daya a wannan hanya da ta yi kaurin-suna da sata. Daga baya dai an ci sa’a wadannan Miyagu sun saki gawar da ake tafe da ita.

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ne ya bada wannan labari a shafinsa na Tuwita. Shehu Sani ya yi wannan magana ne a Ranar Laraba, 8 ga Watan Afrilu, 2020.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun kashe wasu 'Yan fashi da makami a Jihar Kaduna

Birnin Gwari: An yi garkuwa da wadanda su ka dauko Mamaci daga asibitin Shika

Shehu Sani ya ce an sace wasu mutane da gawa daga ABUTH Shika
Source: UGC

Sanata Shehu Sani ya dade ya na kiran gwamnatocin Najeriya su yi wani abu game da wannan daji na Birnin Gwari tun a lokacin da ya ke wakiltar Yankin a majalisar dattawa.

Tsohon Sanatan ya nuna cewa har zuwa daren Ranar Larabar da ta wuce, wadannan Samari su na hannun masu garkuwa da mutane. Kawo yanzu babu labarin kubuto da su.

Haka zalika ‘Dan siyasar bai bayyana kudin fansar da aka daurawa wadannan Samari hudu ba. Samarin sun fito ne daga asibitin koyon aikin Likita da ke Shika a Garin Zariya.

Kwanakin baya mun samu labarin wani Attajiri da aka sace a Garin Kaduna. Duk da an biya Naira miliyan 20, har yanzu ba a sake shi ba, inda masu garkuwar su ka bukaci karin kudi.

Sai dai har yanzu Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da ke Kaduna ba ta tabbatar da aukuwar wannan labari ba kamar yadda ta saba fitowa ta bada rahoto idan an samu irin haka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel