CAN: Gwamnatin Tarayya da MURIC sun juya abin da Bishof Kukah ya fada
- Bishof Mathew Hassan Kukah ya yi wasu maganganu da su ka jawo surutu
- MURIC ta yi kaca-kaca da Mathew Hassan Kukah kan maganar juyin-mulki
- Kungiyar CAN ta fito ta na kare Malamin, ta ce an rikidar da kalaman na sa
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta fito ta kare babban limaminta a Sokoto, Bishof Mathew Hassan Kukah.
Kungiyar ta CAN ta ce a jawabin da Mathew Hassan Kukah ya yi na bikin Kirismeti, babu inda ya soki Musulunci ko kuma ya yi kiran ayi juyin-mulki.
CAN ta zargi gwamnatin tarayya, shugaban kasa da kuma shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da neman juya maganar da Faston ya yi.
Wannan jawabi da CAN ta yi, ya fito ne daga bakin mataimakin shugabanta na duka jihohin Arewacin Najeriya, Rabaren John Hayab jiya a Abuja.
KU KARANTA: Buhari: Dattawan yankin Arewa sun dura kan Mathew Kukah
John Hayab ya ce CAN ta girgiza da yadda gwamnati da kungiyar MURIC su ke yunkurin canza maganar Kukah a lokacin da ake fama da rashin tsaro.
Ya ce: “CAN ba ta ga inda aka nemi a caccaki Musulunci ko kiran ayi juyin-mulki ba, abin takaici, MURIC ta na kokarin hada mutane rikicin addini ne."
Ita kungiyar MURIC ta bakin shugabanta, Akintola, tayi kaca-kaca da Bishof Kukah ta ce kalamansa ba su da linzamni, kuma za su iya tada zaune tsaye.
MURIC ta ce ba za ta bari maganganun da Matthew Kukah ya yi su tafi a haka ba, ta yi Allah-wadai da sakataren na kwamitin zaman lafiya na kasa.
KU KARANTA: Bakare ya yi kaca-kaca da ‘yan adawar Tinubu, Fasto ya yabi Jigon APC
Punch ta rahoto MURIC ta na cewa babu gaskiya a zargin da Kukah yake yi wa Buhari, sai da kurum takaicin abin da ya ke samu a Aso Villa ya yanke.
A makon da ya gabata kun ji cewa wasu kungiyoyi sun yi wa Shugaban kasa kaca-kaca na cewa a yanzu samu zaman lafiya a Borno, Yobe da jihar Adamawa.
Muhammadu Buhari ya furta an samun zaman lafiya a wadannan wurare a mulkinsa, amma kungiyoyin sun yi masa martani, su ka ce sam ba haka ba.
ACF da irinsu CNG sun yi wa Buhari raddi, su ka ce karya kake yi kace an samu zaman lafiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng