Buhari ya batawa manyan Arewa rai da cewa tsaro ya samu a yankin Borno da Yobe

Buhari ya batawa manyan Arewa rai da cewa tsaro ya samu a yankin Borno da Yobe

- Buhari ya fitar da jawabi yana cewa cewa tsaro ya samu a Adamawa, Borno da Yobe

- Ran manyan Arewa ya baci da wannan magana da shugaban kasar ya yi a makon

- Sauran kungiyoyin irinsu CNG, da kuma Middle Belt Forum sun aika da martanoni

Kungiyoyin Arewa Consultative Forum da ta Middle Belt Forum na mutanen yankin Arewa sun fusata da maganar da shugaban kasa ya yi a kan tsaro.

Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya na cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali yanzu a yankunan Borno, Adamawa da Yobe.

Jaridar Punch ta rahoto Coalition of Northern Groups ta gammayar kungiyoyin Arewa ta na cewa babu abin da ke cikin bayanin shugaban kasar sai karya.

Shugaban Middle Belt Forum na kasa, Dr, Bitrus Porgu ya yi magana da ‘yan jarida a Jos, ya ce maganar samar da zaman lafiyan a yankunan karya ce.

KU KARANTA: ‘Dan shekara 44 da aka kama da laifin sace mai shekara 2 zai tafi kurkuku

Ya ce: “Boko Haram suna cigaba da kashe mutanen a wadannan yankuna, Har yau, mutanen Gwoza da Michika da su ka tsere Kamaru ba su dawo ba.”

Kungiyar ta ce an kai hare-hare a Chibok, Michika, Gwoza, Askira, Maiduguri-Damaturu da sauransu.

Sakataren yada labarai na ACF, Emmanuel Yawe, ya girgiza da kalaman shugaban kasar, ya ce babu zaman lafiyan da aka samu a wadannan yankunan.

Emmanuel Yawe ya tunawa jama’a cewa kwanan nan aka kashe manoma a Zabarmari, Borno.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane: ‘Yan bindiga sun fito da Malamin ABU Zaria

Buhari ya batawa manyan Arewa rai da cewa tsaro ya samu a yankin Borno da Yobe
Shugaban kasar Najeriya Hoto: Twitter/@MBuhari
Asali: Twitter

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya ce: “Tuni mutane sun cire tsammani da sa rai daga Buhari da mukarrabansa, ko da su fito sufadi gaskiya ne.”

A yau ake samun labarin cewa wasu yan ta'addan Boko Haram sun kashe mutane shida, sannan sun kona wani coci a karamar hukumar Chibok, jihar Borno.

An yi asarar rayuka, gidaje da motoci a harin da 'yan suka kai, amma jami'an saro sun yi gum.

Suleiman da kungiyarsu ta CNG su na ganin Buhari ya zagaye kansa ne da 'yan amshin-shata da tarin mutanen da ba za su iya fitowa su fada masa gakiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng