Tunde Bakare: Kwarewar Tinubu ta taimaki Buhari, APC a zabukan 2015 da 2019

Tunde Bakare: Kwarewar Tinubu ta taimaki Buhari, APC a zabukan 2015 da 2019

- Fasto Tunde Bakare ya yabi Jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu

- ‘Dan siyasar ya ce Bola Tinubu ya taimaka sosai wajen samun nasarar APC

- Ya ce ba don Tinubu ba, da APC ba za ta iya lashe zabukan 2015 da 2019

Shugaban cocin Citadel Global Community Church, wanda aka sani a baya da Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya yabi Asiwaju Bola Tinubu.

A ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020, aka ji Fasto Tunde Bakare ya na yabon tsohon gwamnan na Legas kuma babban jagoran jam’iyyar APC.

Malamin addinin ya bayyana cewa Ubangiji ya riga ya yi wa Asiwaju Bola Tinubu daukaka, ya ce a sanadiyyarsa APC ta lashe zaben 2015 da 2019 a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an san tsohon abokin takarar na Muhammadu Buhari a CPC da sukar Bola Tinubu, sai kuma aka ji yanzu ya na jinjina masa.

KU KARANTA: Jagoran ‘Yan PDP ya hakikance a kan tsige Shugaba Buhari a Majalisa

A wani jawabi da Fasto Bakare ya yi kwanan nan, ya kamanta ‘dan siyasar da Jephtaph na cikin Injila. Bakare ya kara wa tafiyar ta su Tinubu kwarin-gwiwa.

‘Dan siyasar ya yi kaca-kaca da ‘yan kwaratsin da ke sukar Tinubu duk da ba su kama kafarsa ba, amma ba su da aikin yi sai kokarin jefa zargi a kan nasabarsa.

Faston ya ce sanin sunan mahafiyar Asiwaju ko kuma mahaifinsa ba shi ne zai ceci Najeriya ba.

“Duk da kalubale da gwagwarmayar da ya fuskanta a rayuwa, kamar dai Jephthah, ya hana jam’iyyar PDP iya taba Legas da jihohin yamma a 1999-2007.”

KU KARANTA: Ana so Nnamani ya yi takarar 2023 a jam'iyyar APC

Tunde Bakare: Kwarewar Tinubu ta taimaki Buhari, APC a zabukan 2015 da 2019
Tunde Bakare da Bola Tinubu Hoto: Twitter / @T_Bakare, @AsiwajuTinubu
Source: Twitter

Bakare ya cigaba da cewa: “Idan za a fadi gaskiya, idan ba don hadin-kansa da kwarewarsa ba, da nasarar jam’iyyar APC a zabukan 2015 da 2019 bai taba yiwuwa ba.”

Dazu kun ji cewa Sanata Sir Roland Owie ya tabo maganar zaben 2023, ya ce ya kamata mulki ya koma bangaren Kudu maso gabashin Najeriya a zabe mai zuwa.

Sanata Owie ya ce Ibo su ka dace da mulki ba mutanen bangaren Yarbawa ko Neja-Delta ba.

A dalilin haka ne Sir Owie ya roki Asiwaju Bola Tinubu ya janye takara, ya bar Ibo su taba shugabanci a karon fari tun da aka dawo mulkin farar hula a 1999.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel