Dattawan arewa sun yi martani ga kiran Kukah na yiwa gwamnatin Buhari juyin mulki
- Dattawan arewa basu ji dadin sakon Kirsimeti da Bishop Kukah ya saki ba inda ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Buhari
- Babban faston na Sokoto ya zargi shugaban kasa da son kai, cewa idan da wata kabilar ce tayi haka, da Najeriya ta kasance cikin yaki
- A martaninta, kungiyar NEF ta ce duk wanda baya farin ciki da gwamnatin Buhari toh ya tafi kotu
Bishop na cocin Katolika da ke Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya sha caccaka kan sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi a sakonsa na Kirsimeti.
Kungiyar dattawa arewa ta NEF ta ga laifin malamin kan cewa da yayi a tsige Shugaban kasar ta tsarin da baya bisa damokradiyya.
Kukah a martaninsa kan hare-hare da kasha kashe da ake yi a kasar, ya ce idan da Musulmin da ba dan arewa bane Shugaban kasa sannan ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi juyin mulki da dadewa.
KU KARANTA KUMA: Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri
Kungiyar ta NEF a martaninta tace koda dai ta yarda da maganar Kukah na cewa gwamnatin Buhari bata mutunta wasu abubuwa, ba daidai bane neman mafita ga matsaloli ta tsarin da ya saba damokradiyya, jaridar This Day ta ruwaito.
A cewar Dr. Hakeem Baba-Ahmed, daraktan kungiyar, Najeriya na fuskantar kalubale a karkashin Buhari ta bangaren zartar da hukunci.
Sai dai, ya ce kungiyar bata goyon bayan kowani irin gwamnati baya ga wanda aka samu bisa takarkin damokradiyya.
A cewarsa, mafi akasarin mutane, hatta ga wadanda ke goyon bayan shugaban kasar, na burin ina ma ace yana ba da muhimmanci sosai wajen zabar wadanda yake ba mukami.
Sai dai kuma, Baba-Ahmed ya kara da cewa duk wani dan kasa da baya farin ciki da gwamnatin Buhari to ya nemi gyara a kotu.
KU KARANTA KUMA: Hadiza Gabon ta gwangwaje tsohon da yace yana sonta
A wani labarin, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba.
Gwamnan ya je Abuja don aiwatar da wasu jerin ayyuka amma sai ya takaita tafiyar sannan ya koma jiharsa a safiyar ranar Lahadi.
Harin na ranar Asabar ya shafi akalla garuruwa hudu da suka hada da Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro. Hatta ga makarantu, shaguna da wuraren bauta basu tsira ba a harin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng