Daruruwan mutane sun tsere yayinda dakarun soji ke fafatawa da Boko Haram a kauyukan Borno

Daruruwan mutane sun tsere yayinda dakarun soji ke fafatawa da Boko Haram a kauyukan Borno

- Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hare-hare a jihohin Zamfara da Borno a yayin wannan biki na Kirsimeti

- Sai dai dakarun sojin Najeriya basu yi masu ta dadi ba yayinda suka yi musayar wuta da sun a tsawon sa’o’i masu yawa

- Hakan ya tursasa mazauna kauyukan da abun ya shafa tserewa zuwa saman tsaunuka inda suke kallon fafatawar

Mayakan Boko Haram basu ji ta dadi ba a karshen makon nan yayinda dakarun Operation Lafiya Dole suka fafata da su tsawon sa’o’i a karamar hukumar Hawul da ke jihar Borno.

Mazauna kauyukan basu da wani zabi da ya wuce tserewa saman tsaunuka sakamakon musayar wuta da aka dungi yi sannan suka nemi mafaka a jejin da ke kusa.

A bisa ga rahoton jaridar This Day, har a lokacin kawo wannan rahoton ana nan ana fafatawa tsakanin dakarun sojin da mayakan a kauyuka uku da ke karamar hukumar Hawul.

Daruruwan mutane sun tsere yayinda dakarun soji ke fafatawa da Boko Haram a kauyukan Borno
Daruruwan mutane sun tsere yayinda dakarun soji ke fafatawa da Boko Haram a kauyukan Borno Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Dattawan arewa sun yi martani ga kiran Kukah na yiwa gwamnatin Buhari juyin mulki

Ku tuna cewa mayakan Boko Haram a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba sun kai farmaki karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno. Daga cikin garuruwan da abun ya shafa sune, Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro.

A cewar kakakin rundunar sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, rundunar Operation Lafiya Dole na sama sun yi amfani da jirgin yaki wajen fafatawa da maharan.

Ya ce:

“Jirgin yaki na ta fafatawa da yan ta’addan Boko Haram.”

Wani dan kungiyar sa kai a yankin ya bayyana cewa maharan sun kona cocin EYN da ke Tashan Allade.

KU KARANTA KUMA: Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

Wani dan JTF, Balami Yusuf, ya fada ma manema labarai cewa har yanzu yan ta’addan na kaddamar da hare-hare a wasu kauyukan.

An tattaro cewa hare-haren dakarun sojin saman ya tursasa yan ta’addan tserewa.

A gefe guda, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba.

Gwamnan ya je Abuja don aiwatar da wasu jerin ayyuka amma sai ya takaita tafiyar sannan ya koma jiharsa a safiyar ranar Lahadi.

Harin na ranar Asabar ya shafi akalla garuruwa hudu da suka hada da Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro. Hatta ga makarantu, shaguna da wuraren bauta basu tsira ba a harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel