- Matasan Arewa sun bi sahun sauran kungiyoyi don yin martani a kan furucin Bishop Kukah game da gwamnatin Shugaba Buhari
- Kungiyar matasan bata tsaya ga Allah-wadai da furucin malamin ba kadai, ta yi kira ga kama shi da kuma hukunta shi
- Bishop din na Katolika a Sokoto ya zargi gwamnatin Buhari da son kai da kuma gazawa
- A cewar kungiyar Arewan, furucin Kukah na tunzurawa ne da cin amanar kasar Najeriya
Kungiyar matasan Arewa ta AYCF ta bayyana furucin Bishop Mathew Kukah na baya-bayan nan a matsayin kokarin karfafa yin juyin mulki.
A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Yerima Shettima, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba, zuwa ga Legit.ng, kungiyar ta ce hakan tayar da fitina ne kan zababbiyar gwamnatin damkradiyya ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ku tuna cewa Kukah a sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, ya zargi Shugaban kasa Buhari da son kai.

Kungiyar Arewa ta nemi a kama Kukah sannan a hukunta shi kan furucinsa game da Buhari
Source: Original
Da suke nuna rashin jin dadinsu kan furucin, AYCF ta ga laifin Kukah da yayi amfani da son kai a matsayin makamin bata kan gwamnati da mutanen Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari, ya dauki tsatsauran mataki
Kungiyar arewar na so a kama malamin sannan ya fuskanci hukunci kan abunda ta bayyana a matsayin cin amanar kasar Najeriya.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya Kukah cikin mutanen da za a dunga kula da duk wani motsinsu kan yunkurin kawo hargitsi a kasar ta hanyar hada kudu da arewa rigima.
Shettima a jawabin, ya bayyana abunda Kukah yayi a matsayin aikin shaidan a yayinda arewa ke fafutukar dawo da zaman lafiya da daidaita tsaro a yankin da Najeriya.
A cewarsa, a wannan lokaci, Najeriya na bukatar shawara mai kyau da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ba wai furucin da zai tunzura matsalolin kasar ba.
KU KARANTA KUMA: Daruruwan mutane sun tsere yayinda dakarun soji ke fafatawa da Boko Haram a kauyukan Borno
A gefe guda, mun ji cewa Kukah, ya sha caccaka kan sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi a sakonsa na Kirsimeti.
Kungiyar dattawa arewa ta NEF ta ga laifin malamin kan cewa da yayi a tsige Shugaban kasar ta tsarin da baya bisa damokradiyya.
Kukah a martaninsa kan hare-hare da kasha kashe da ake yi a kasar, ya ce idan da Musulmin da ba dan arewa bane Shugaban kasa sannan ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi juyin mulki da dadewa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng