Rashin tsaro: An kashe Dr. M.B Hassan a hanyar dawowa aiki daga Jihar Zamfara
A ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2020, aka samu labarin cewa wasu miyagu sun bindige Mohammed Bello Hassan, wani malami a jami’ar Ahmadu Bello da ke garin Zariya.
Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kashe Dr. Mohammad Bello Hassan ne a kan titin Zamfara zuwa Katsina yayin da ya ke dawowa daga wani aiki da aka tura sa.
Mohammad Bello Hassan kwararren malami ne a bangaren tattalin aikin noma a jami’ar, kuma jami’i a cibiyar binciken harkar noma ta IAR da ke Samaru, garin Zariya, jihar Kaduna.
Ana zargin cewa ‘yan bindiga sun bude masu wuta a hanya ne da nufin su yi garkuwa da su. A sanadiyyar haka Mohammed Hassan ya rasa ransa a cikin mota da safiyar ranar Laraba.
Direban da ya ke tare da shi a mota ya tsira, amma ba mu iya samun damar tuntubarsa ba.
Dr. M.B Hassan bai dade daga sauka daga kan kujerar shugaban sashen wayar da kan manoma a tsangayar aikin gona ta jami’ar ba. Marigayin mutumin kirki ne kuma mai sha’awar aiki.
KU KARANTA: Mataimakin Shugaban Jami'ar BUK, Farfesa Wakili ya cika
M.B Hassan ya yi digrinsa na farko a bangaren aikin gona, sai kuma digiri na biyu a bangaren tattalin arzikin harkar noma shekaru da-dama da su ka wuce a jami’ar ta ABU Zariya.
Marigayin ya samu digirinsa na PhD a wannan bangare da ya kware ne a jami’ar KwaZulu-Natal a kasar Afrika ta Kudu. Tun shekarar 2005 ya ke aiki a matsayin malami a jami’ar tarayyar.
An kawo gawarsa ne da kimanin karfe 12:00 na rana a jiya. Kuma an bizne ne shi da yammacin ranar Laraban a gidansa da ke Zariya kamar yadda mu ka samu labari daga abokan aikinsa.
A cikin ‘yan makonnin nan, malamai akalla uku su ka rasu a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, daga ciki akwai; Dr. M. D Ahmed, Dr. Baba Shuaibu Aduku da kuma shi Dr. M. B Hassan.
Kafin yanzu jami’ar ta rasa tsohon shugaban cibiyar IAR, Farfesa A.M Falaki wanda ‘yan sanda su ka bude masa wuta bisa tunanin cewa ya na tare da ‘yan ta’addan Boko Haram a 2015.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng