'Yan bindiga sun sace ɗaliban ABU Zaria 17 a hanyar Kaduna zuwa Abuja
- Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria guda 17
- Ɗaliban suna kan hanyarsu ta zuwa Legas ne don samun horaswa a wata cibiyar koyon harshen Faransanci
- Rahoton ya ce ƴan bindiga sun harbi ɗalibi guda ɗaya da ya yi yunƙurin tserewa sannan sun ƙyale mace ɗaya mai jinjiri
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria su 17 a babban titin Kaduna zuwa Abuja.
The Abusites, jaridar jami'ar ne ya ruwaito afkuwar lamarin a ranar Litinin.
A cewar rahoton, waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin daliban aji 3 ne a tsangayar koyar harshen Faransanci da ke hanyarsu na zuwa Legas don hallartar shirin koyon harshen Faransanci a Nigerian French Language Village, NFL.
DUBA WANNAN: Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya
The Abusites ta ruwaito cewa waɗanda aka yi garkuwa da su a ranar Lahadi sun haɗa da: Okafor Grace, Kyenpia Bulus, Dickson Afolabi, Jemimah Badmus, Aliyu S. Adamu, Simnom Praise, Ziya Asoji, Elizabeth John, Victor Agbo da Precious Mutum.
Kafar watsa labaran ta ce ta samu labarin sace ɗaliban daga wata ɗaliba da ke NFL, Precious Owunna wacce ta wallafa labarin a shafin ta na Twitter don janyo hankalin ƴan Najeriya.
KU KARANTA: Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki
Precious ta rubuta: "Barkan ku da warhaka, Ban san ta yadda zan faɗa muku ba amma muna buƙatar addu'o'in ku, an yi garkuwa da abokai na da abokan karatu na a hanyar Kaduna-Abuja."
Precious, ɗalibar Jami'ar UNN da ke hallartar horaswa a Badagry ta shaidawa The Abusites cewa an harbi ɗalibi ɗaya da ya yi yunƙurin tserewa sannan an saki mace ɗaya domin tana da jinjiri.
A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng