Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya warke daga cutar Korona

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya warke daga cutar Korona

- A rana guda, gwamnonin Najeriya biyu sun samu waraka daga cutar Korona

- Yayinda gwamnan Plateau ya samun waraka da safe, Sanwo-Olu na Legas ya samu da rana

Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya samu waraka daga cutar COVID-19 bayan sake gwajin da akayi masa.

Makut Macham, diraktan yada labaran gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a garin Jos.

Lalong ya kamu da Korona ne ranar 17 ga Disamba.

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya warke daga cutar Korona
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya warke daga cutar Korona
Source: UGC

KU KARANTA: A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

A wani labarin kuwa, alkaluma akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Mutane 1133 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 80,9222 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 69,274 yayinda 1236 suka rigamu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel