An nemi Bala Mohammed ya shiga tseren shugaban kasa a 2023

An nemi Bala Mohammed ya shiga tseren shugaban kasa a 2023

- An bukaci Gwamna Bala Mohammed ya duba yiwuwar fitowa tseren kujerar shugaban kasa a 2023

- Wata kungiya a Abuja ce ta shawarci gwamnan na Bauchi a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin

- An bayyana Bala Mohammed a matsayin shugaba mai tarin sani wanda ka iya cimma mafarkin kasar

Wata kungiyar jama’a ta gamayyar matasa da mata, ta yi kira ga Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi da ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Kungiyar ta yi kiran ne a cikin wata takarda da ta saki a karshen taronta a Abuja, a ranar Litinin dauke da sa hannun Aminu Zakari da Christiana Jacob, shugaba da sakatariyar kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shahararren malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Ahmed Lemu ya rasu

An nemi Bala Mohammed ya shiga tseren shugaban kasa a 2023
An nemi Bala Mohammed ya shiga tseren shugaban kasa a 2023 Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

A cewar kungiyar, zuwa 2023, Najeriya za ta kasance cikin tsananin bukatar shugaba mai gaskiya da cancanta domin jagorantar harkokin kasar.

Har ila yau kungiyar ta ce yan Najeriya na bukatar shugaba da zai kare kasar daga hargitsi da durkushewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Wasu yan siyasa na yi wa Buhari bita da kulli, fadar shugaban kasa

A wani labarin, wasu jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su shida a karamar hukumar Oyibo da ke jihar Ribas, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Hakan na zuwa ne duk da rikicin da ya rincabe a jam’iyyar, sakamakon dakatar da wasu yayanta da aka yi, jaridar The Nation ta ruwaito.

Masu sauya shekar, Adolphus Nweke, Onyema Ihenna, Ibekwe Okere, da sauransu, sun ce PDP ba jam’iyya mai inganci bace.

A gefe daya kuma, Kungiyoyin da ke goyon bayan Ken Nnamani a kasashen ketare, sun yi kira ga Sanata Ken Nnamani ya yi takarar kujerar shugaban kasa.

Wadannan magoya baya suna ganin cewa na-su ne ya fi dacewa ya nemi mulki daga kasar Ibo.

Jaridar Vanguard ta rahoto wadannan kungiyoyi suna cewa Ken Nnamani ya fi kowa dacewa da kujerar shugaban kasa saboda irin kwarewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel