Wasu manyan jiga-jigan PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Ribas

Wasu manyan jiga-jigan PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Ribas

- Jam’iyyar APC a jihar Ribas ta sake karfi yayinda ta tarbi sabbin masu sauya sheka daga PDP

- Jiga-jigan PDP shida a karamar hukumar Oyibo da ke jihar ta kudu maso kudu sun bar jam’iyyar zuwa APC a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba

- Sabbin mambobin sun samu tarba daga shugabancin APC a karamar hukumar Oyibo

Wasu jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su shida a karamar hukumar Oyibo da ke jihar Ribas, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Hakan na zuwa ne duk da rikicin da ya rincabe a jam’iyyar, sakamakon dakatar da wasu yayanta da aka yi, jaridar The Nation ta ruwaito.

Masu sauya shekar, Adolphus Nweke, Onyema Ihenna, Ibekwe Okere, da sauransu, sun ce PDP ba jam’iyya mai inganci bace.

Wasu manyan jiga-jigan PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Ribas
Wasu manyan jiga-jigan PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Ribas Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Suna burin cewa tsarin jam’iyyar zai kara karfi bayan wannan lokaci da ake ciki na rikice-rikice.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shahararren malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Ahmed Lemu ya rasu

“Mun gwammaci mu zamo yayan APC masu tasiri da kuma kasancewa cikin masu aiki, fiye da ace muna amsa babban suna da mutuwa cikin kangin rayuwa,” in ji su.

Masu sauyin shekar sun samu tarba a ranar Laraba daga shugaban jam’iyyar a Oyibo, Gift Okere da kuma shugaban kwamitin rikon kwarya, Chamberlain Okorie.

Okorie ya bayyana cewa PDP a Oyibo ta rushe sakamakon sauyin shekar da manyan jiga-jiganta suka yi zuwa APC. Ya bukaci sabbin mambobin da su yi aiki don nasarar APC a zabe na gaba.

Ya yi kira garesu kan bukatar hadin kai da kwazon aiki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar, yayinda ya basu tabbacin samun babban garabasa a karkashin jagorancin ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

KU KARANTA KUMA: Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu

Okorie ya yi zargin cewa babu wasu ayyukan gwamnati a yankin duk da irin kwazo da jajircewar masu sauyin shekar a lokacin da suke PDP.

A wani labarin, jagoran ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP, Kingsley Chinda, ya ce babu wanda zai ba hakuri saboda ya fito ya na cewa a sauke shugaban kasar Najeriya.

A ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020, jaridar Punch ta rahoto ‘dan majalisar ya na cewa akwai yunkurin da ake yi na sauke shugaban kasar.

Kingsley Chinda, ya ce jam’iyyar PDP ta na wayar da kan ‘yan majalisar tarayya da sauran mutanen kasa domin kawo maganar tsige shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel