2023: Wata Kungiya ta na so Ken Nnamani ya yi takarar Shugabancin Najeriya

2023: Wata Kungiya ta na so Ken Nnamani ya yi takarar Shugabancin Najeriya

- Wasu su na burin ina ma Sanata Ken Nnamani ya karbi mulkin Najeriya

- Magoya bayan ‘Dan siyasar su na ganin shi ya fi cancanta ya gaji Buhari

- Nnamani, Tsohon ‘Dan Majalisa ne wanda yanzu ya na cikin manyan APC

Kungiyoyin da ke goyon bayan Ken Nnamani a kasashen ketare, sun yi kira ga Sanata Ken Nnamani ya yi takarar kujerar shugaban kasa.

Wadannan magoya baya suna ganin cewa na-su ne ya fi dacewa ya nemi mulki daga kasar Ibo.

Jaridar Vanguard ta rahoto wadannan kungiyoyi suna cewa Ken Nnamani ya fi kowa dacewa da kujerar shugaban kasa saboda irin kwarewarsa.

Kungiyoyin sun kawo aikin da Nnamani ya yi a baya a majalisa, inda ya tsaya tsayin-daka wajen ganin an hana Olusegun Obasanjo sake zarcewa.

KU KARANTA: Tsohon Sanatan APC ya soki sabuwar dokar Ganduje

Shugaban wannan tafiya, Lawrence Odoemelam ya fitar da jawabi, ya na cewa Ibo su na burin ‘dan cikin su ya samu mulkin Najeriya a zaben 2023.

Mista Lawrence Odoemelam ya ce wanda ya dace da wannan kujera daga cikin Inyamurai shi ne Nnamani saboda wadannan dalilan da ya ambata.

Ya ce Nnamani ya taimaka wajen kafuwar mulkin farar hula, kuma ya nuna kwarewar shugabanci, sannan ya na cikin masu goyon-baya.

Odoemelam ya na ganin idan gwanin na su ya karbi shugabancin kasar nan a 2023, za a mulki ‘Yan Najeriya da bin dokar kasa, adalci, da gaskiya.

KU KARANTA: “Idan Gwamnonin APC sun isa, su kaddamar da aikin da su ka yi a Jihohinsu"

2023: Wata Kungiya ta na so Ken Nnamani ya yi takarar Shugabancin Najeriya
Sanata Ken Nnamani Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

A 2003 ne Nnamani ya zama Sanata inda har ya yi nasarar zama shugaban majalisar dattawa tsakanin 2005 har zuwa karshen gwamnatinsu a 2007.

A makon nan kun ji cewa an sake shafe wata da watanni, matar Shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ba ta zaune a cikin fadar Aso Villa.

Ana rade-radin rashin tsaro ya sa Aisha Muhammadu Buhari ta dauki tsawon watanni ba ta tare da mai gidanta, amma hadimin ta ya ce lafiya ta je nema.

Uwargidar Najeriya Aisha Buhari ta tafi Dubai tun watannin baya, har yau ba ta dawo gida ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel