Yanzu Yanzu: Shahararren malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Ahmed Lemu ya rasu

Yanzu Yanzu: Shahararren malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Ahmed Lemu ya rasu

- Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Lemu, ya rasu

- Sheikh Lemu ya rasu ne da sanyin safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba

- Marigayin ya yiwa addinin Musulunci sosai a lokacin da yake raye

Allah ya yiwa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.

Shehin malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba a garin Minna, babbar birnin jihar Niger.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Yanzu Yanzu: Shahararren malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Ahmed Lemu ya rasu
Yanzu Yanzu: Shahararren malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Ahmed Lemu ya rasu Hoto: Kingfaisalprize.org
Source: UGC

Daya daga cikin yayan marigayin, Maryam Lemu, ta tabbatar da mutuwar mahaifinsu a wata sanarwa a Facebook, ta ce idan anjima kadan za a soma shirye-shiryen binne shi.

Sheikh Dr. Lemu shahararren masani, ya kasance mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga yiwa musulunci hidima.

KU KARANTA KUMA: Wasu yan siyasa na yi wa Buhari bita da kulli, fadar shugaban kasa

Hakazalika mutum ne mai kira ga yin masalaha da sassauci a tsakanin al'umma da kuma bayyana ra'ayinsa akan al'amura ba tare da rufa-rufa ba.

Sheikh Lemu ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen kare hakkin mata, haka kuma ya kafa kungiyar Da'awa domin yaki da tsattsauran ra'ayi.

A wani labarin, mun ji cewa mutanen garin Azare a jihar Bauchi sun shiga alhini sakamakon mutuwar Sarkin Dawakin Katagum, Alhaji Muhammad Lele Mukhtar.

Mukhtar, wanda ya kasance tsohon sakataren dindindin na tarayya ya rasu ne a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

Marigayin basaraken ya yi aiki a matsayin kwamishina na kasa, hukumar tsare-tsare ta kasa (NPLC) kuma mamba a majalisar FJSC.

A gefe guda kuma, Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja a jihar arewa maso yamma, ya rasu, lamarin da ya jefa Gombe cikin halin juyayi.

Tsohon gwamnan na mulkin soja ya rasu a ranar Juma’a, 18 ga watan Disamba.

Ya yi aiki a matsayin gwamna a mulkin soja a jihar ta arewa maso yamma daga 1967 zuwa 1975 bayan an wareta daga tsohuwar yankin arewa a mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel