Wasu yan siyasa na yi wa Buhari bita da kulli, fadar shugaban kasa

Wasu yan siyasa na yi wa Buhari bita da kulli, fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta ce akwai shirye-shirye da wasu mutane ke yi don shafa wa shugaba Buhari da gwamnatinsa bakin fenti

- Femi Adesina, kakakin shugaban kasar ya koka a wata sanarwa a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba

- Adesina ya yi kira ga yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan rahoton musamman daga yanar gizo

Fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, ta koka a kan shirin da wasu yan siyasa ke yi na bata sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ofishinsa.

A cewar wata sanarwa da kakakin Shugaban kasa, Femi Adesina ya wallafa a shafin Facebook, ya ce akwai wani makirci da ake shiryawa don bata wa Shugaban Najeriyan bakin fentin cewa ba shine ke rike da ragamar kasar ba.

Kakakin Shugaban kasar a cikin sanarwar ya bayyana cewa wadanda ke shirya wannan munakisar suna bi ta hannun wadanda ke fada aji a yanar gizo a matsayin madogara.

Wasu yan siyasa na yi wa Buhari bita da kulli, fadar shugaban kasa
Wasu yan siyasa na yi wa Buhari bita da kulli, fadar shugaban kasa Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Ya ci gaba da bayyana cewa a kwanaki masu zuwa mutanen na shirin yin wasu zarge-zarge a kan Shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Karo na biyu: Ba za mu rufe Plateau ba, in ji Lalong

Adesina ya kara da cewa kudirin wadanda ke shirya wannan munakisar shine shafa wa Shugaban kasar bakin fenti tare da haddasa hargitsi a kasar.

Kakakin Shugaban kasar yayinda yake bukatar yan Najeriya da su kula da irin labaran da suke ji ya bukaci jama’a da su yi taka-tsantsan da irin wannaan rahoton.

Ya bayyana cewa Shugaban kasar na ci gaba da myar da hankali ga jajircewarsa na yi wa yan Najeriya hidima iya bakin iyawarsa kuma ba zai bari a janye masa hankali ba.

KU KARANTA KUMA: Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu

A wani labarin, a ranar Laraba ma’aikatan jami’an gwamnatin Najeriya wadanda ba su koyarwa su ka gargadi gwamnati game da kudin da ta ke shirin biyan ASUU.

Kungiyoyin SSANU, NASU da NAAT na malaman fasaha da sauran ma’aikata jami’o’i su na kukan akwai rashin adalci wajen yadda za a raba wannan kudi.

Kafin ASUU ta janye yajin-aiki yau, sai da gwamnati ta yi alkawarin biyan jami’o’i Naira biliyan 40 a matsayin alawus din karin aikin da ake jibga masu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel