Gwamna Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin jihar Kano na shekarar 2021

Gwamna Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin jihar Kano na shekarar 2021

- Abdullahi Umar Ganduje ya amince da kasafin kudin N177b na shekara mai zuwa

- Gwamnatin Kano ta ware kaso mai tsoka wajen harkar ilmi da kuma kiwon lafiya

- Abin da gwamnan ya yi kasafi na badi bai kai abin da aka kashe shekarar bana ba

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya rattaba hannunsa a kan kasafin kudin jihar na shekara mai zuwa, Daily Trust ta bada wannan rahoto.

Jaridar ta fitar da rahoto a ranar 23 ga watan Disamba, 2020, cewa mai girma Dr. Abdullahi Ganduje ya sa hannu a kan kasafin N177, 936, 730, 540.

Kudin da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano su ka amince a batar a shekarar badi bai kai abin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kashe a 2020 ba.

Annobar Coronavirus da ake fama da ita a Duniya ce ta yi sanadiyyar raguwar kudin batarwar.

KU KARANTA: Ganduje ya caccaki masu sukar Gwamnatinsa

Duk da haka gwamnatin Ganduje tana ganin cewa jihar Kano ba za ta gamu da cikas a gudanar da tsare-tsare da aiwatar da ayyukan da ta sa a gaban ta ba.

Ya ce: “Ba girman kasafin kudin ba ne abin dubawa, aikin da kasafin zai yi da kuma damar tattaro kudin da za mu ci karfin 90% na ayyukan da mu ka ware.”

Gwamnatin Kano za ta maida hankali ne wajen harkar ilimi, kiwon lafiya da abubuwan more rayuwa a wannan kasafi aka yi wa take da kasafin gar-da-gar.

“Mu na son gina dakin shan magani daya a kowace mazaba 448 a jihar.” Inji Gwamnan da yake son ganin an aiwatar da 90% na ayyukan da aka ware a badi.

KU KARANTA: A mutu ko ayi rai: Kwankwaso ya fito da iyalinsa - APC

Gwamna Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin jihar Kano na shekarar 2021
Gwamna Umar Ganduje Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Domin rage yawan fita zuwa Birane, za mu inganta asibitocin da ke cikin duka masarautunmu, ya zama su na iya daukar gadon marasa lafiya akalla 400."

A yau ne mu ka ji tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya na kaca-kaca da Abdullahi Ganduje, ya zama lauyan tsohon Sarki Muhammdu Sanusi.

Rabiu Kwankwaso ya ce karya gwamna Ganduje yake yi a game da abin da ya sa ya tsige Sarkin, ya ce babu abin da ya hada tsige Sanusi II da Goodluck Jonathan.

A cewarsa fadar gaskiya da kiyayya ga masarauta su ka jawo gwamna ya tunbuke Sanusi II.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel