Masu suka ta 'yan kauye ne, in ji gwamnan Kano Ganduje

Masu suka ta 'yan kauye ne, in ji gwamnan Kano Ganduje

- Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Jihar Kano, ya ce masu sukar matakin da gwamnatinsa ta dauka kan wasu kamfanoni kauyawa ne

- Gwamnan Ganduje ya yi wannan furucin ne kan sauya ginin Triump da Daula Hotel zuwa wasu sabbin gine-gine

- Gwamnan ya ce wadanda ke suka abinda gwamnatinsa ta yi kauyawa ne kuma ba su yi binciken yadda zamani ke tafiya ba kafin tsoma baki kan batun

Gwamnan Jihar Kano Abdulllahi Ganduje ya bayyana masu sukar yadda gwamnatinsa ta sarrafa wasu gine-gine ciki har da Daula Hotel a matsayin kauyawa marasa hangen nesa, Vanguard ta ruwaito.

Ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke duba Birnin Tattalin Arzikin Kano da aka kashe biliyoyin naira wurin ginawa da ke Dangwauro a kan Zaria road kusa da birnin Kano da yammacin Talata.

Masu suka ta 'yan kauye ne, in ji gwamnan Kano Ganduje
Masu suka ta 'yan kauye ne, in ji gwamnan Kano Ganduje
Asali: UGC

Da ya ke karin bayani a kan ayyukan gwamnatin Jihar Kano, Ganduje ya ce baya ga sayar da ginin Triump Newspapers da aka fi sani da Gidan Sa'adu Zungur, an sauya ginin zuwa kasuwar canjin kudade na zamani.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

"Wadanda ke sukan mu ba su fahimci cewa aikin jarida na zamani baya bukatar babban gini domin wallafa jarida ba hakan yasa zamu mayar da ginin kasuwar canjin kudade na zamani.

"Masu canjin kudade na WAPA za su koma ginin kuma 'yan kasuwan mu da dama za su amfana da wannan cigaban," in ji gwamnan.

Ya kara da cewa wadanda ke sukarsa ba su fahimci yadda aikin jarida na zamani ke tafiya ba inda ya bukaci su rika bincike kafin tsoma bakinsu cikin batu.

"Wannan ya nuna sun jahilci yadda ake aikin jarida na zamani. Ya kamata a tunatar da mutane cewa gwamnatin da ta shude ne ta tilastawa jaridar Triump dena aiki kuma an dade da rufe kamfanin kafin mu zo mulki.

KU KARANTA: 2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

"Don haka su wane ke da laifi, wadanda suka kashe kamfani ko kuma wadanda suka fahimci muhimmancin ta suka dawo da shi," ya tambaya.

Da ya ke magana game da wani kamfanin, Dauula Hotel, Ganduje ya ce kamfanin ya tsufa kuma baya tafiya da zamani. Don haka, zabin da ya rage wa gwamnati shine ta fara amfani da shi.

A wani rahoton daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164