Kano: A janye maganar hana mota daukar fasinjoji a Sabon Gari inji Shehu Sani
- Shehu Sani ya soki wata doka da Gwamnatin Jihar Kano ta kawo
- An hana duk masu manyan motoci ajiye fasinjojinsu a Sabon Gari
- Tsohon Sanatan ya roki Gwamnatin Kano ta janye wannan dokar
Sanata Shehu ya yi magana game da sabon tsarin da gwamnatin jihar Kano ta kawo, wanda masu harkar manyan motoci su ke kuka da shi.
Kwanaki Gwamnatin jihar Kano ta sa masu tuka manyan motoci su bar tashar Sabon Gari, su koma ajiye fasinjojinsu a hanyar Maiduguri.
Shehu Sani ya bayyana cewa wannan doka da Mai girma Dr. Abdullahi Ganduje ya kawo ta sabawa dokar kasa, don haka ya nemi a soke ta.
Ga abin da Sanata Sani ya rubuta a shafinsa na Twitter:
KU KARANTA: Zaben 2023 sai dai mu mutu a Kano - Kwankwaso
“Ya gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ka janye matakin da ka dauka na canzawa masu harkar manyan motoci wuri na daina sauke fasinjoji a tashar Sabon Gari, su koma babban hanyar zuwa garin Maiduguri.”
Tsohon ‘dan majalisar dattawan ya kuma roki gwamnatin Kano ta cire harajin Naira miliyan 10 da ake rade-radin za a rika karba kan masu saba dokar.
Ya ce: “Idan sauran jihohi su ka fara yin haka, an yi watsi da dokar da ta halatta zirga-zirga.”
Kawo yanzu gwamnatin Abdullahi Ganduje ba ta maida martani ba, kuma babu sanarwar an janye wannan dokar lodi ko kuma harajin da aka shigo da shi.
KU KARANTA: Idan Gwamnonin APC sun isa, su nuna aikin da su ka yi - Wike
Tuni dai kungiyar ALBON ta masu manyan motoci su ka nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan shi ya tsoma baki game da dokar da aka kawo.
Masu aikin manyan motoci sun ce wannan doka da aka kawo ta na wahalar da su a wajen aiki, a lokacin da ‘yan kasuwa ke neman agajin gwamnatin kasar.
Dazu kun ji labarin yadda wasu Miyagu su ka kashe Jami’in tsaro bayan sun sace Baiwar Allah da ‘dan jaririnta a cikin karamar hukumar Rogo, da ke jihar Kano
A lokacin da ake fama da matalsar rashin tsaro a yankin Arewacin Najeriya, ‘Yan bindiga sun shiga yankin dajin Falgore, sun yi ta’adi cikin duhun tsakar dare.
‘Yan bindiga fiye da 50 su ka dura Kauyen Falgore da daren jiya, su ka ce wannan mata da 'danta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng