Ganduje ya nada mahaifin Kwankwaso dan majalisar nadin sarakunan Karaye

Ganduje ya nada mahaifin Kwankwaso dan majalisar nadin sarakunan Karaye

- Gwamnatin Jihar Kano ta yi sabbin nade nade a masarautar karamar hukumar Karaye

- Wani jami'i daga karamar hukumar Karaye ya bayyana cewa sabbin wadanda aka yi wa nadin za su fara aiki a ranar Juma'a 27 ga watan Nuwamba

- A halin yanzu jihar Kano tana da masarautu guda biyar da sarakuna masu daraja ta daya suke jagoranta

An nada Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan Kano a matsayin dan majalisar nadin sarakuna a masarautar Karaye ta Jihar Kano.

Ganduje ya nada mahaifin Kwankwaso a matsayin mai zaben Sarki a masarautar Karaye
Ganduje ya nada mahaifin Kwankwaso a matsayin mai zaben Sarki a masarautar Karaye. Hoto: @jrnaib2
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon direkta ya tsallake rijiya da baya yayinda 'yan bindiga suka afka musu a Abuja

Mai magana da yawun masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 26 ga watan Nuwamban kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Gunduwawa ya ce a ranar Juma'a 27 ga watan Nuwamba ne za a rantsar da Saleh Kwankwaso wadda dama ke rike da sarautar 'Makaman Karaye' a matsayin dan majalisar sarki.

KU KARANTA: Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere

Masarautar Karaye na cikin sabbin masarautu hudu da gwamnatin Jihar Kano ta kirkira karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar 5 ga watan Disamban 2019.

Dokar da Ganduje ya rattaba wa hannu ta bada damar bawa sarakunan hudu matsayin daraja ta farko wadda suka hada ba Bichi, Karaye, Rano da Gaya.

Jim kadan bayan kirkirar sabbin masarautun ne aka tsige gwamnan Kano, Muhammadu Sanusi II.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso yana daga cikin wadanda ba su goyi bayan kirkirar sabbin masarautun ba.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164