Yan bindiga sun sace dagaci da mutum 15 a kauyen Katsina

Yan bindiga sun sace dagaci da mutum 15 a kauyen Katsina

- Yan bindiga sun sace mai unguwa da wasu mutane 15 a kauyen Kaigar Malamai da ke Jihar Katsina

- Cikin wadanda aka sace akwai matan aure shida, sai 'yan mata uku da kuma kananan yara guda uku

- Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Isah Gambo ya ce zai bincika ya tabbatar da gaskiyar lamarin

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a daren ranar Litinin sun sace dagacin kauyen Kaigar Malamai, a karamar hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina tare da wasu mutane 15.

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa 'yan bindigan masu yawa sun afka kauyen a daren ranar Litinin inda suka ci karensu ba babbaka na tsawon awanni kafin suka tafi da wadanda suka sace.

Yan bindiga sun sace dagaci da mutum 15 a kauyen Katsina
Yan bindiga sun sace dagaci da mutum 15 a kauyen Katsina. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

"Sun kai hari kauyenmu, Unguwar Malamai, misalin karfe 11:45 na dare suka fara harbe harbe.

"Sunyi awon gaba da mutane 16 ciki har da dagacin kauyen, Maiunguwa Kabir, matan aure shida, 'yan mata uku da yara shida.

"A lokacin, mutum uku cikin yan bindigan ya tilastawa daya daga cikin mutanen ya kai su gidan yayansa, a kan babur dinsa, kuma ya aikata hakan. Biyu daga cikinsu suka shiga gidan daya kuma da ya tsaya daga kofa ya fada wa mutumin ya tsere.

KU KARANTA: Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna)

"Da ya tsere daga wurin, ya tafi wurin jami'an tsaro ya fada musu abinda ke faruwa a kauyen amma a maimakon su tafi su tunkari 'yan bindigan sai suka fada masa ya tsaya a wurinsu ya kwana," in ji majiyar.

Mai magana da yawun 'yan sandan Jihar, SP Isah Gambo, ya ce bai riga ya tabbatar da afkuwar abin ba amma ya yi alkawarin zai kira sai dai bai kira ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164