2023: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a Kano, ba zamu yarda da 'inconclusive' ba, Kwankwaso
- Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar PDP ya gargadi jam'iyyar APC game da zaben 2023 mai zuwa
- Kwankwaso ya ce shi da magoya bayansa ba za su sake amince da zaben 'inconclusive' ba don wannan karon sai dai 'a mutu ko a yi rai'
- Kwankwaso ya zargi jam'iyyar APC da hadin baki da INEC, hukumomin tsaro da wasu manyan mutane wurin murde zaben 2019 amma ya ce ba za ta yi wa a sake hakan a 2023 ba
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargadi jam'iyyar APC a jihar cewa PDP ba zata sake amincewa a maimaita mata 'inconclusive' kamar yadda aka yi a zaben shekarar 2019 ba.
Sanata Kwankwaso ya ce shi da jam'iyyarsa na PDP da magoya bayansa 'yan Kwakwasiyya, ba za su amince a sake maimaita hakan ba, Premium Times ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria
A 2019, PDP na kan gaba a zaben gwamna a Kano kafin hukumar zabe, INEC, ta ce zaben bai kammalu ba. Daga bisani aka yi zaben raba gardama a wasu yankuna kuma APC ta yi nasara, hakan ya bawa gwamna Abdulllahi Ganduje nasarar zarcewa kan mulki.
Kwankwaso ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis, yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi inda suka rika jinjina masa.
Daga bisani an wallafa bidiyon jawabin a shafin Facebook na Kwankwasiyya da aka saba wallafa labaran siyasa masu alaka da jigon na PDP.
A cikin bidiyon, da Kwankwaso ya yi magana da harshen Hausa, ya ce: "Yanzu sun bugu da giyyar mulki ba su tunanin sauka daga mulki domin suna tunanin 2023 ba zai zo ba.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama wasu da suka yi yunƙurin fashi da bindigar roba a Legas
"A tunaninsu, dukkan zunuban da suka aikata, za su hada baki da hukumar INEC da jami'an tsaro a 2023 da wasu shugabanni su maimaita zaben inconclusive da suka yi a Kano a 2019 kuma mu kyalle su.
"2023 zai banbanta da baya, sai dai a mutu ko a yi rai, za mu shirya musu.
"A 2023, ina kira ga mata su dakko tabarya da ludayin miya su rike kusa da su (don kare kuri'ansu)," Kwankwaso ya furta yayin da ake masa jinjina.
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.
Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.
Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng