‘Yan Sanda sun tabbatar da satar Mai goyo da jaririnta a Rogo, Jihar Kano

‘Yan Sanda sun tabbatar da satar Mai goyo da jaririnta a Rogo, Jihar Kano

- ‘Yan bindiga sun sace wata mata da jaririnta a Garin Falgore a farkon makon nan

- An kashe wani mutumi daga cikin wadanda su kayi yunkurin kai wa iyalin dauki

- Miyagun sun shiga cikin karamar hukumar Rogo ne da tsakar dare a kan babura

Wasu da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne sun hallaka wani jami’in tsaron ‘dan-sa-kai a garin Falgore, karamar hukumar Rano, a jihar Kano.

Jaridar Premium Times tace ‘yan bindigan sun yi wannan ta’adi ne bayan sace wata mata da ke shayarwa, sun hada har da jaririnta, sun yi gaba.

Shugaban karamar hukumar Rogo, Malami Rogo, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo masu ne a tsakar daren ranar Lahadin nan da ta wuce.

Rogo ya ce ‘yan bindigan sun shiga gidan wani Alhaji Yusuf Falgore, su kayi wannan aika-aika.

KU KARANTA: APC tana so Obaseki ya sauka daga mulki saboda rashin tsaro

Jami’an tsaro sun yi yunkurin ceto mutanen nan da aka sace, amma wadannan miyagu sun kashe guda daga cikin ‘yan sa-kan da su ka bi sawu.

Tuni aka yi wa mamacin sutura, aka birne shi yadda addini ya tanada, kamar yadda shugaban karamar hukumar na Rogo ya shaidawa ‘yan jarida.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a garin mai iyaka tsakanin jihar Katsina da Kano.

Wani ma'aikacin BBC Hausa, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari, ya ce daga cikin wadanda aka kashe har da wani direban ‘yan sanda.

KU KARANTA: Miyagun ‘Yan bindiga sun kashe mutane 14 a sa’a 48 a Kaduna

‘Yan Sanda sun tabbatar da satar Mai goyo da jaririnta a Rogo, Jihar Kano
Gwamna Ganduje na Jihar Kano Hoto: www.rfi.fr/ha/najeriya
Source: UGC

Wannan majiya ta ce ‘yan bindiga fiye da 50 su ka shiga garin Falgore a kan baburansu. An ga wadannan miyagu ne tsakanin karfe 1 zuwa 3 na dare.

Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai, Femi Adesina yace rashin tsaro ya ragu a Najeriya domin yanzu bam sun daina tashi kamar lokacin baya.

Da ya ke magana a kan tsaro, Hadimin shugaban kasar ya ce an daina ruwan bam duk ranar Allah da zuwan shugaba Muhammadu Buhari kan mulki a 2015.

Fadar Shugaban kasar ta yi magana ne bayan an kai hari 5 a kwana 2 a wasu jihohin Arewa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel