Gwamna Wike ya caccaki APC yayin da ya kammala aikin wasu hanyoyi a GRA

Gwamna Wike ya caccaki APC yayin da ya kammala aikin wasu hanyoyi a GRA

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kalubalanci takwarorinsa da ke jam’iyyar APC, su nuna irin ayyukan da su ke yi wa mutanensu.

Jaridar Vanguard ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun nuna su na kaunar jama’a ta hanyar yin aiki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar wajen kaddamar da hanyoyi uku da gwamnatin Ribas ta yi a karkashin PDP.

Samuel Ortom ya kaddamar da titin Tombia, Ndoni da Amaji, a cikin sabuwar GRA, Phase 2 da ke karamar hukumar Obio/Akpor, a Ribas.

KU KARANTA: Zulum ya karrama wasu Sojoji

A cewar Nyesom Wike, gwamnonin da ke jam’iyyar PDP ne kadai su ka dage wajen kawowa jihohinsu ayyukan cigaba da more rayuwa.

“Kwanakin baya, gwamnan Benuwai ya gayyace ni domin kaddammar da wasu ayyuka. Na je, na kaddamar da tituna akalla uku.” Inji Wike.

Wike ya ce sun samu karbuwa wajen mutanen Benuwai, don haka ya yi alkawarin gayyatar gwamnansu domin maida alherin da aka yi masa.

Gwamnan adawan ya ce: “Mu na kalubalantar jam’iyya mai mulki ta fito da ayyukan da su ka yi, su gayyaci mutane su zo su kaddamar da su."

KU KARANTA: Buhari ya hadu da Namadi Sambo

Gwamna Wike ya caccaki APC yayin da ya kammala aikin wasu hanyoyi a GRA
Nyesom Wike Hoto: twitter.com/GovWike/status/1341425048532504576
Asali: Facebook

“Abin da ya sa na gayyaci gwamnan Benuwai shi ne in nunawa jama’a cewa akwai mutanen da su ke kokarin aiki domin cigaban kasar nan.”

Dazu kun ji cewa gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun yi ganawar sirri da gwamnan Katsina.

Gwamnonin sun samu ganawa da gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari a gidan gwamnatinsa a kan yawan satar jama'a da ake yi a yankin Arewa.

Shugaban NGF, ya ce matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso yamma ta na da hadari sosai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel