Femi Adesina ya ce ‘ayi murna’ da ake shafe kwana da kwanaki babu labarin bam

Femi Adesina ya ce ‘ayi murna’ da ake shafe kwana da kwanaki babu labarin bam

- Femi Adesina ya ce ya kamata mutane su zama masu godiya ga Allah yanzu

- Fadar shugaban kasa tace an yi lokaci a da, da bam-bamai suke tashi kullum

- Adesina yace da Buhari ya hau mulki an samu raguwar tashin bam a Najeriya

Fadar shugaban kasa ta yi kira ga mutanen Najeriya su godewa Allah da aka daina samun tashin bama-bamai kamar yadda aka saba yi a baya.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya maida martani game da kukan da ‘yan Najeriya su ke yi game da sha’anin tsaro.

Mista Femi Adesina ya bayyana ne a shirin siyasa na Sunday Politics a gidan talabijin na Channels. Punch ta fitar da wannan rahoto dazu.

Adesina yace kafin zuwan mai gidansa shugaba Muhammadu Buhari kan mulki, akwai lokacin da sai bama-bamai har shida su tashi a rana guda.

KU KARANTA: Rashin tsaro: PDP da APC su na rikici a kan Gwamna Obaseki

Hadimin shugaban kasar yace kashe-kashen da ake yi a kasa ya ragu da zuwan Muhammadu Buhari.

A cewar Hadimin, yanzu bam ba su tashi a Najeriya domin ana shafe watanni da makonni ba tare da an samu aukuwar wannan mummunan lamari ba.

Mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya maida martani ne game da mabambantan hare-hare biyar da aka kai a kwanaki uku da suka wuce.

“Yanzu sai a samu biyu, ayi watanni uku ba tare da an samu tashin bam ba, Mu gode da wannan saukin da aka samu, duk saukin da aka samu, mu gode.”

KU KARANTA: Miyagun ‘Yan bindiga sun kashe mutane 14 a Garuruwan Kaduna

Femi Adesina ya ce ‘ayi murna’ da ake shafe kwana da kwanaki babu labarin bam
Femi Adesina da shugaban kasa Hoto: web.facebook.com/femi.adesina
Source: Facebook

“Idan an yi kwanaki babu mummunan labari, mu maida hankali a kan wannan.” Inji Adesina.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin Neja-Delta, Ita Enang, ya ce Gwamnonin jihohin Neja-Delta su ke da laifi wajen rashin tsaro da ake samu.

Sanata Ita Enang ya bayyana cewa Jihohin da ke da arzikin danyen mai sun yi wasa da karin 13% da su ke samu daga asusun gwamnatin tarayyar Najeriya.

Tsohon Sanatan ya zargi Gwamnoninsu da wasa da damar da suka samu na kawo cigaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel