Mutum 4 sun mutu a danyen harin ‘Yan bindiga a Kudancin jihar Kaduna
-Miyagu sun kai hara-hare a garuruwan Kauru, Lere da kuma Zangon-Kataf
-An rasa rai a Ungwan Gaiya, Ungwan Gimba, Ungwan Makama da Apimbu
-Gwamnatin Kaduna tace an rasa ran mutum 14 daga Alhamis zuwa Asabar
Mutane hudu, daga ciki har da wasu makiyaya sun mutu a wani hari da aka kai a cikin wasu kauyukan garin Zangon-Kataf, jihar Kaduna.
A ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020, Punch ta rahoto cewa an yi ta’adi a Ungwan Gaiya, Ungwan Gimba, Ungwan Makama da Apimbu.
Kwamishinan harkoki da tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi da yamma.
Mista Aruwan ya yi wa jawabin da ya fitar take da: “An kashe mutane hudu a harin ramuwar gayya, yayin da aka baza dakaru a wuraren rikici.”
KU KARANTA: Enang ya zargi Gwamnonin Neja-Delta da wasa da damar da suka samu
A cewar Kwamishinan, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kira a bar doka ta yi aikinta.
Tsakanin ranar Alhamis zuwa daren Asabar, ‘yan bindiga sun hallaka akalla mutane 14 a kananan hukumomi uku; Zango-Kataf, Kauru da Lere.
Rahoton yace wadanda aka yi wa rauni suna jinya a asibiti, yayin da aka kona gidaje kurmus.
Kwamishinan yace jami’an sojoji da ‘yan sanda sun tabbatar masu cewa an kai harin ne a matsayin ramuwar gayya na kashe-kashen da aka yi.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Abin da ya sa mu ka ce Obaseki ya yi murabus – APC
A garuruwan Unguwan Idi da Kasheku a karamar hukumar Kauru, an kashe makiyaya bakwai a harin. Bayan nan, an kashe wani mutum a yankin Apimbu.
Jami’an tsaro sun samu gawar mutane uku a Unguwan Gaiya, Ungwan Gimba da Unguwan Makama, ba a iya gane fuskar daya daga cikinsu ba.
A makon jiya mun kawo rahotan dalla-dallar hanyar da aka bi, aka saki yara na makarantar GSSS Kankara, jihar Katsina 340 daga hannun ‘Yan bindiga.
Lai Mohammed ya ce sun samu gudumuwa daga waje kafin a iya kubuto da ‘Yan Makarantar.
Bayan haka, gwamnatin Najeriya tace ko sisinta bai yi ciwo ba, Lai Mohammed yace babu maganar kudi a yarjejeniyar da aka shiga ‘da Yan bindigan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng