Hisbah ta kama mutane 43 da laifin tallata kayan barasa da zaman kansu inji Ibn-Syna
- Dakarun Hisbah sun kama mutane da ake zargi da saida giya da kwayoyi
- An kuma kama wasu mata masu cutar HIV da suke zaman kansu a Kano
- Shugaban dakarun Hisbah ta Kano Harun Ibn-Syna ne ya tabbatar da haka
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane 43 da zargin laifin zaman kansu da kuma saida kayan barasa da suka sabawa shari'a.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama masu saida giyan ne a kasuwar kayan marmari ta Kwanar Gafan dake karamar hukumar Garun Malam.
Jaridar Daily Nigerian ce ta fitar da rahoto a jiya ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020.
Shugaban dakarun Hisbah, Dr. Harun Ibn-Syna, ya gabatar da wadanda aka kama da zargin aikata wadannan laifuffuka jiya a unguwar Sharada.
KU KARANTA: Hisbah ta kama 'Dan Sanda mai sace yara, ya yi lalata da su
“Daga cikin mutane 43 da aka cafke, 34 mata ne, ragowar maza tara ne masu shekaru 15 zuwa 18.”
Dr. Ibn-Syna ya ce: “Binciken da aka gabatar a kan wadanda ake zargin ya nuna a cikin mazan akwai takwas da ke saida miyagun kwayoyi.”
“Daya kuma an same shi da kwalaye 80 na kwalaben giya.” Inji Ibn-Syna. A jihar Kano mai amfani da shari’ar musulunci, cinikin giya bai halatta ba.
Shugaban dakarun Hisbah na jihar Kano yace an samu 14 daga cikin matan da ke zaman kansu su na dauke da kwayar cutar HIV watau kanjamau.
KU KARANTA: HISBAH ta na bi lungu da sako domin cafke masu badala
Bayan haka an samu bororon roba na maza da mata a kasuwar. Hisbah ta hada kai da hukumar NDLEA na kasa ne wajen gudanar da wannan aiki.
A watannin baya kun ji labarin yadda kotu ta ce a kamo mata wasu shugabannin hukumar HISBAH a jihar Sokoto saboda kin amsa kiran Alkali.
Wata kotun shari’a da ke zama a garin Tudun Wada, karamar hukumar Sokoto ta kudu, ta bada umarnin cafke shugaban hukumar Hisbah na Sokoto.
An zargi jami’an hukumar shari'ar da laifin tsare mutane ba tare da bin doka ba, da bata masu suna.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng