Hisbah ta kama dan sandan da ke sace yaran mutane domin lalata da su a Kano
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani Basiru a wani gida yana lalata da wata yarinya mai karancin shekaru
- Mahaifin yarinyar ya ce ya nemi yarinyar sama ko kasa bai ganta ba na tsawon kwana 2, ashe tana wurin Basiru
- Hukumar ta na neman har da abokinsa, Jamilu, wanda ya gina gida musamman don yin lalata da mata
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani dan sanda Basiru a wuraren Rumawa da ke karamar hukumar Ungogo a kan laifin lalata, Vanguard ta wallafa.
Kamar yadda hukumar tace, an kama har da Basiru abokin Jamilu a wani daki da ke wuraren Rumawa, inda suka boye suna aikata alfashar.
Mazauna Rumawa sun yi gaggawar sanar da yadda Basiru da abokin sharholiyarsa suka makale a wani daki suna lalata da wata yarinya mai karancin shekaru, wacce iyayenta suka yi ta neman ta amma basu ganta ba.
KU KARANTA: A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur
Marikin yarinyar, Usman Ahmad ya ce ya yi ta neman diyarsa bai ganta ba, sai daga baya ya gano tana hannun hukuma.
"Basiru, abokin Jamilu ya gina gida a Rumawa musamman don yin lalata da kananan yara da sauransu.
"Na kan nemi yarinyata kwana biyu in rasa ta. Wannan karon na nemeta na kwana 2 ban ganta ba, ashe tana dakin wadannan mutanen," cewar marikinta.
Ya kara da cewa, "an kama Basiru da Jamilu, mai gidan da ake lalatar. Sannan an mayar da al'amarin a hannun 'yan sanda don su cigaba da bincike."
KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta janye belin Faisal Maina, ta bukaci a damko shi
A wani labari na daban, wani mutum mai suna Olumuyiwa Johnson, mai yara 2, ya tabbatar wa da wata kotu da take Ibadan cewa ba zai iya zama da matarsa ba.
A cewarsa, aurensa mai shekaru 24 ya kare da matarsa saboda rashin kamun kanta da barazana ga rayuwarsa.
Olumuyiwa, wanda mazaunin wuraren Eleta ne a Ibadan, ya tabbatar wa da alkali Ademola Odunade, cewa matarsa tana barazana ga rayuwarsa bayan ya gano tana lalata da wasu kusoshin cocinsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng