Sokoto: Kotu ta ce a kamo Shugabannin HISBAH saboda kin amsa kiran Alkali

Sokoto: Kotu ta ce a kamo Shugabannin HISBAH saboda kin amsa kiran Alkali

Jaridar Daily Trust ta rahoto kotun shari’a da ke zama a garin Tudun Wada, karamar hukumar Sokoto ta kudu, ta bada umarnin cafke shugaban hukumar Hisbah na jihar Sokoto.

Alkali kotun shari’an ya bada damar kama shugaban HISBAH da Alkalin hukumar na reshen Sokoto ne a dalilin kin amsa gayyatar da aka yi masu a gaban kotu.

Rahoton ya bayyana ana zargin jami’an biyu da laifin tsare mutane ba tare da bin doka ba. Sauran zargin da ke kansu su na da alaka da rikicin aure da cin mutunci da bata suna.

Caliphate Trust ta fahimci cewa wasu Bayin Allah; Hadiza Abubakar da Habibu Bawa ne su ka kai karar jami’an na HISBAH a kotu a dalilin wasu hukunci da hukumar ta yanke masu.

Hadiza Abubakar wanda ta rabu da mai gidanta ta zargi Alkalin hukumar da rashin gaskiya a dalilin mika ‘dan da ta haifa zuwa ga mijinta alhali yaron bai cika shekaru biyu ba.

Bayan haka Hadiza Abubakar ta na karar Alkalin HISBAH da laifin ci mata mutunci da tsare ta na tsawon mako guda ba tare da wani dalili ba, wanda ta ce hakan keta mata alfarma ne.

KU KARANTA: Tagwaye sun haifi tagwaye bayan sun auri tagwaye

Sokoto: Kotu ta ce a kamo Shugabannin HISBAH saboda kin amsa kiran kotu
Kotun shari'a a Najeriya
Asali: UGC

Bazawarar ta shaidawa ‘yan jarida ta samu matsala da jami’an hukumar ne bayan sabani ya shiga tsakaninta da mai gidanta inda aka rufe ta har sai da tsohon mijinta ya nemi a bada belinta.

Bayan ta samu beli, HISBAH ta sake cafke ta, aka tsare ta na kwana biyu, sannan aka raba ta da ‘danta. Ta ce an ba ta N40, 000 a matsayin kudin shayarwa, wanda ta ki karba.

Shi kuma a na sa bangaren, Habibu Bawa ya ce an tsare shi ba tare da hakki ba, kuma aka tursasa masa sakin mai dakinsa, sannan aka zarge shi da laifuffukan da bai san da su ba.

“Sun kira ni ofis cewa surukai na sun kawo kara ina zargin mata ta da aikata alfasha, don haka su ka nemi takarda, sai Alkalin hukumar ya bukaci a biya ni N30, 000 in rubuta saki.” inji Bawa.

Da aka tuntubi shugaban HISBAH, Dr. Adamu Bello Kasarawa, ya ce sun daukaka kara zuwa babban kotu. Shi ma Alkakin hukumar, Ibrahim Rufa’i ya musanya zargin da ake yi masa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel