An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama

An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama

- A ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, an dakatar da ministan sufuri, Rotimi Amaechi daga jam’iyyar APC

- Shugaban riko na APC a jihar, Igo Aguma shine ya yanke hukuncin dakatar da Amaechi

- Aguma ya bayyana cewa an yanke hukuncin ne a taron shugabannin jam’iyyar na musamman a Port Harcourt

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Igo Aguma a jihar Ribas, ta dakatar da Rotimi Amaechi, ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa dakatarwar ya zurfafa rikicin jam’iyyar reshen jihar, inda ta kara da cewa dukkanin sansanonin biyu na fafutukar samun ikon jan ragamar APC gabannin zaben 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa bangaren Amaechi na jam’iyyar sun kaddamar da dakatar da tsohon sanata, Magnus Abe, Igo Aguma, Livingstone Wecchie, Wogu Boms da dukkanin shugabannin rikon kwarya da Aguma ya rantsar a karshen mako.

An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama
An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: 2023: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a Kano, ba zamu yarda da 'inconclusive' ba, Kwankwaso

Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, a wata sanarwa dauke da sa hadimin labaransa, Livingstone Wechie, ya ce APC ta rubuta wasika ga hukumar zabe ta jihar Ribas domin kaddamar da shirinta na shiga zaben karamar hukuma mai zuwa a jihar.

Ya bayyana cewa an zartar da hukuncin dakatar da Amaechi daga jam’iyyar a wajen taro na musamman karkashin jagorancin Aguma a Port Harcourt, babbar birnin jihar.

Wechie ya kara da cewar taron ya samu halartan manyan mambobin jam’iyyar, wadanda suka hada kai wajen yanke manyan hukunce-hukunce kan abubuwan da ke addabar ta.

Jawabin ya ce "kwamitin rikon kwaryan ya aiwatar da shawarar kwamitin da’a na jam’iyyar a jihar wanda ya duba hukuncin gudunma da karamar hukuma wajen dakatar da Amaechi, wanda ya fito daga gudunma ta 8, karamar hukumar Ikwerre kan yin ayyukan da suka saba wa jam’iyya."

KU KARANTA KUMA: Majalisa za ta hukunta mamba dan PDP akan kiran a tsige Buhari, jam'iyya ta ce babu ruwanta

A gefe guda, mun kawo a baya cewa Kwamitin riko na jam'iyyar APC a jihar Ribas ya sanar da dakatar da Magnus Abe, tsohon Sanata mai wakiltar Ribas ta arewa maso gabas.

Shugaban kwamitin riko na APC a jihar Ribas, Isaac Ogbula, ne ya sanar da hakan yayin taronsa da manema labarai a Ribas.

Bayan Sanata Abe, jam'iyyar ta sanar da dakatar da tsohon shugabanta na riko, Livingstone Nweche, da tsohon kakakinta da tsohon kwamishinan shari'a, Wogu Boms.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng