APC ta dakatar da Sanata Abe da sauran wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar

APC ta dakatar da Sanata Abe da sauran wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar

- Rikicin shugabancin jam'iyyar APC a jihar Ribas ya kara rincabewa

- An gaza cimma daidaito da fahimtar juna a tsakanin tsagin da ke biyayya da Amaechi da mai biyayya ga Sanata Abe

- Shugaban riko na APC a jihar Ribas, Isaac Ogbubula, ya sanar da dakatar da Sanata Abe da wasu jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar

Kwamitin riko na jam'iyyar APC a jihar Ribas ya sanar da dakatar da Magnus Abe, tsohon Sanata mai wakiltar Ribas ta arewa maso gabas.

Shugaban kwamitin riko na APC a jihar Ribas, Isaac Ogbula, ne ya sanar da hakan yayin taronsa da manema labarai a Ribas.

Bayan Sanata Abe, jam'iyyar ta sanar da dakatar da tsohon shugabanta na riko, Livingstone Nweche, da tsohon kakakinta da tsohon kwamishinan shari'a, Wogu Boms.

DUBA WANNAN: Waken suya zai sa yaranku su kara tsayi; in ji kwararriya a kimiyyar abinci

Jaridar Newswire ta rawaito cewa shugabancin da ya dakatar da Sanata Abe mai biyayya ne ga ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

APC ta dakatar da Sanata Abe da sauran wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar
APC ta dakatar da Sanata Abe da sauran wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar
Asali: Twitter

An dade ba'a ga maciji a tsakanin Amaechi da Sanata Abe a kan shugabanci da tafiyar da al'amuran jam'iyyar APC a jihar Ribas.

DUBA WANNAN: AFENIFERE: Satar daliban Kankara da kubutar da su duk damfara ce

A jawabin da ya gabatar, Ogbubula ya ce mazabun da mutanen suka fito sun bayar da shawarar cewa a koresu daga jam'iyyar.

Sai majalisar gudanarwa ta uwar jam'iyya (NEC) ta amince da hakan kafin hukuncin ya tabbata.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa an fara 'yar fallashe tsakanin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da wasu tsofin kwamishinoninsa.

Gwamna Wike ya fusata ne bayan kwamishinonin sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin kasa.

Tsofin kwamishinonin sun mayar da martani a kan kalaman Wike na zarginsu da satar kudin gwamnati a lokacin da suke rike da mukamansu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel