Majalisa za ta hukunta mamba dan PDP akan kiran a tsige Buhari, jam'iyya ta ce babu ruwanta

Majalisa za ta hukunta mamba dan PDP akan kiran a tsige Buhari, jam'iyya ta ce babu ruwanta

- Mamba a majalisar wakilai kuma dan jam'iyyar PDP, Kingsley Chinda, zai fuskanci hukuncin ladabtarwa

-Honarabul Kingsley ya shiga tsaka mai wuya ne sakamakon kiran da ya yi na cewa a tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari

- Dan majalisar ya ce shugaba Buhari ya gaza samar da tsaro a yankin arewa kuma ya ki amsa kiran majalisa domin yin jawabi a kan halin da tsaron kasa ke ciki

Wani dan Majalisar wakilai ta tarayya na gab da shiga tsaka mai wuya sakamakon kiran da ya yiwa majalisar da ta tsige shugaban ƙasa bisa gazawa wajen samar da tsaro a Najeriya.

Dan majalisar wakilan, Kingsley Chinda, mai wakiltar Obia/Akpor kuma ɗan jam'iyyar PDP, ya bukaci da a tsige shugaba Muhammadu Buhari ranar 7 ga Disamba biyo bayan yankan rago da yan kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma a Zabarmari.

Kazalika, ya ce bai kamata a bar batun kin bayyanar da shugaban kasar ya yi a zauren Majalisar don karin bayani kan taɓarbarewa tsaro ta wuce haka ba, kamar yadda ChannelsTV ta rawaito.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Majalisa za ta hukunta mamba dan PDP akan kiran a tsige Buhari, jam'iyya ta ce babu ruwanta
Majalisa za ta hukunta mamba dan PDP akan kiran a tsige Buhari, jam'iyya ta ce babu ruwanta @HouseNGR
Asali: Twitter

Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Alasan Ado Doguwa, ya bayyana wannan kiran da cewa sam baya kan tsari kuma rashin ta-ido ne da ganin kimar shugaban ƙasar.

Kazalika, mambobin PDP a zauren majalisar sun ce babu ruwansu, honarabul Kingsley ya bayyana ra'ayinsa ne kawai ba na jam'iyya ba.

KARANTA: Korona: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai, da Cocinan Kaduna

A dan haka ne shugaban masu rinjaye na Majalisar ya sha alwashin cewa majalisa sai ta hukunta duk wani ɗanta da ya kaucewa tsarin majalisar.

Ana iya cewa dai, Kingsley Chinda, na gab da fuskantar hukuncin ladabtarwa bisa kiran da ya yi na tsige shugaban sakamakon taɓarbarewa tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim Pius Anyim, ya ce sai mutanen yankin kudu maso gabashin kasar nan, na 'yan kabilar Igbo, sun sauya halayyarsu kafin su samu takarar kujerar shugaban kasa.

Sanata Anyim, ya yi wannan iƙirari ne a wani biki mai taken World Igbo Summit, wanda jami'ar Gregory dake Uturu a jihar Abia ta shirya a karo na shida, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Cikin bayaninsa mai taken, "Duban tsanaki kan buƙatar ƙabilar Igbo ga mulkin ƙasar nan tare da tsarin cimma hakan," Anyim ya nuna giɓin dake akwai na ɓallewa ko sauya tsarin fasalin ƙasar nan.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel