Yadda Gwamnonin Neja-Delta suke kawo matsalar rashin tsaro inji Ita Enang

Yadda Gwamnonin Neja-Delta suke kawo matsalar rashin tsaro inji Ita Enang

- Ita Enang ya zargi Gwamnonin Neja-Delta da azalzala wutar rikicin yankin

- Sanata Enang yace Gwamnonin Jihohi suka sa ake samun rikici a Neja-Delta

- Hadimin Shugaban kasar yace al’ummar ba su amfana da karin kason 13%

Babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin Neja-Delta, Ita Enang, ya yi magana game da harkar rashin tsaro.

Sanata Ita Enang ya zargi gwamnonin jihohin yankin Neja-Delta da kasa a gwiwa wajen samar da tsaro.

A yau ne jaridar Daily Trust ta rahoto hadimin shugaban kasar yana zargin gwamnonin jihohi masu arzikin fetur da rashin kawo zaman lafiya.

Sanata Enang ya bayyana haka ne yayin da kungiyar DROAN ta masu matatar danyen mai a Najeriya suka kai masa wata ziyara a ofishinsa.

KU KARANTA: Zaben 2023: Inyamurai sun sha alwashin ganin Ibo a Aso Villa

Kara karanta wannan

ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoninsu a Yankunan Zamfara, Gwamnatin Jiha ta Koka

Yadda Gwamnonin Neja-Delta suke kawo matsalar rashin tsaro inji Ita Enang
Ita Enang Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Enang ya ce: “Gwamnonin sun yi sanadiyyar da yankunan da ke da danyen mai ba za su zaunu ba,” Ya ce a dalilin haka ake da matsalar rashin tsaro.

Da yake jawabi a gaban ‘ya ‘yan kungiyar DROAN, Enang ya ce karin kason kudin da ake ba yankin sam bai yi amfani wajen kawo cigaba ba.

Ya ce: “Gwamnonin bangaren Neja-Delta sun kawo matsalar rashin tsaro saboda kin amfani da kason 13% wajen kawowa yankunansu cigaba.”

A dokar kasa, ana ware karin kudi na musamman wajen rabon kason FAAC, wanda ake ba duk wata jiha da ta ke da arzikin man fetur a Najeriya.

KU KARANTA: Zaman ASUU da Gwamnati ya dauki tsawon lokaci, ana sauraron matsaya

Yadda Gwamnonin Neja-Delta suke kawo matsalar rashin tsaro inji Ita Enang
Sanata Ita Enang Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mai ba shugaban kasa shawara, Ita Enang, ya taba rike kujerar Sanata a Akwa Ibom, jihar da ta fi kowace arzikin mai a kasa, kafin ya koma APC.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

Manyan jihohin Neja-Delta su ne Ribas, Bayelsa da Delta, sai kuma irinsu Akwa Ibom, Kuros Riba, Edo da bangarorin Abia, Imo da kuma jihar Ondo.

The core states are Rivers, Bayelsa, and Delta, where most of our work is focused, with some activities in the surrounding states of Akwa Ibom, Cross River, and Edo. Sometimes the states of Abia, Imo, and Ondo are also included in the definition of the Niger Delta region.

Mun samu labari daga majiyar fadar shugaban kasa a kan ainihin abubuwa da suka sa Muhammadu Buhari ya hakura, ya bude iyakoki.

Annobar Coronavirus, tashin farashin kaya, duk su na cikin dalilan da suka tursasa Gwamnati tayi amai ta lashe wajen bude iyakokin tudun kasar.

Ministar kudi ta shawo kan shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da bude iyakoki hudu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel